Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Hadarin jirgi: Amurka ta ki dakatar da amfani da jiragen  ‘Boeing 737 Max’

Xaya daga cikin ‘yan Najeriya da suka rasu a haxarin Farfesa Pius Adesanmi

Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Amurka ta bayyana cewa kasar ba za ta dakatar da amfani da jirgi kirar ‘Boeing 737 Max’ ba, duk da irin wutar da aka huro mata daga bangaren sanatoci da kuma kungiyoyin ma’aikatan kasar.

Hukumar ta bayyana cewa an yi bita a kan yanayin aikin jirgin kuma ba a gano wata matsala tattare da shi ba, saboda haka babu hujjar dakatar da amfani da samfurin jiragen.

ADVERTISEMENT

Ted Cruz dan Jam’iyyar Republican wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Sufurin Jiragen Sama na Majalisar Dattawan  Amurka ya ce, “Ina ganin ya kamata Amurka mu yi tunani domin dakatar da amfani da wannan jirgi har sai Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta tabbatar da ko za a iya amfani da jirgin domin ci gaba da daukar fasinja ba tare da wata matsala ba.”

Haka ma ’yan Jam’iyyar Democrats da suka hada da Edward Markey da Richard Blumenthal sun rubuta wa hukumar ta Amurka inda su ma suka yi irin wannan bukata ta Sanata Ted Cruz.

ADVERTISEMENT

Amma a nata bangaren, hukumar ta ce sauran hukumomi masu sa ido a kan lafiyar jiragen sama a kasar ba su yi wani sahihin bayani ba da zai zama hujjar dakatar da amfani da jirgin ba.

A ranar Lahadi ce wani jirgi na kasar Habasha ya yi hadari inda mutum 157 suka rasa ransu da suka hada da fasinja 149 da ma’aikata takwas kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Fasinja 32 da ke cikin jirgin ’yan kasar Kenya ne, sai 18 ’yan Kanada, da takwas ’yan Amurka, sai kuma bakwai ’yan Birtaniya da biyu ’yan Najeriya.

Wannan hadarin ya auku ne watanni biyar bayan irin samfurin jirgin na kasar Indonisiya ya yi hadari.

A yanzu haka kasashe da dama da suka hada da Birtaniya da kasashen Tarayyar Turai da Austireliya sun dakatar da amfani da wannan jirgi bayan hadari na biyu da ya yi a ranar Lahadin kamar yadda BBC ya rawaito.

Sannan a shekaraniya Laraba, Hong Kong da Bietnam da New Zealand suka shiga jerin kasashen da suka dakatar da amfani da samfarin jirgin na 737 Max.

Hadarin jirage a bara

Jirgi qirar Boeing 737 Max

Domin waiwaye a kan hadarin jirgin sama, BBC ya kalato hadarurrukan da suka auko a bara kamar haka:

Ranar 29 ga Oktoba: Jirgin sama kirar Boeing 737 Mad, mallakar Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Lion Air ya yi hadari a tekun Jaba jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta na kasar Indonesiya.

Daukacin fasinja 189 da matukan jirgin duk sun mutu, kuma wani mai aikin ceton sa-kai da ke iyo a ruwa shi ma ya hallaka.

Masu bincike sun ce jirgin na da matsala a cikin injinsa, wanda kamata ya yi a dakatar da tashinsa har sai an shawo kan matsalar.

18 ga Mayu: Jirgi kirar Boeing 737 mai daukar fasinja ya yi hadari, inda ya rikito jim kadan da dagawarsa daga babban filin jiragen sama na Jose Marti da ke Habana kasar Kyuba, inda ya hallaka mutum 112.

11 ga Afirilu: Jirgin sama ya yi hadari jim kadan bayan dagawarsa a kusa da babban birnin Aljeriya na Aljers, wanda ya hallaka daukacin fasinja 257 da ke cikinsa, wadanda suka hada da matukansa 10. Mafi yawan wadanda suka mutu sojoji ne da iyalansu.

12 ga Maris: Wani jirgin sama mai daukar fasinja 71 da matukansa ya yi hadari wajen saukarsa a filin jirgin sama na Kathmandu na kasar Nepal. Mutum sama da 50 ne suka mutu lokacin da jirgin kirar Bombadier Dash 8 turboprop ya fadi.

18 ga Fabrairu: Wani jirgin fasinja ya yi hadari a tsaunukan Zagros da ke kasar Iran, inda daukacin fasinja 66 suka hallaka. Jirgin mallakar Kamfanin Sufuri na Aseman Mad Airlines ATR Jirgin kirar ‘turboprop’ ya yi hadarin ne kimanin sa’a guda bayan tashinsa daga Babban Birnin kasar, Tehran lokacin da ya nufi birnin Yasuj da ke Kudu maso Yammacin kasar.

11 ga Fabrairu: Wani jirgin fasinjan Rasha ya yi hadari mintuna kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Domodedobo da ke Mosko tare da fasinja 71, jirgin kirar Antonobo An-148, mallakar Kamfanin Sufuri na Orsk ya yi hadarin ne a tsaunukan Ural, a kauyen Argunobo, kimanin kilomita 80 (mil 50) da ke Kudu maso Gabashin Mosoko.