✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin jirgin sama ya kashe mutane da dama a Kongo

Mahukunta sun ce akalla mutum 24 ne suka rasu bayan da wani jirgin sama ya fada kan wasu gidaje a garin Goma da ke gabashin…

Mahukunta sun ce akalla mutum 24 ne suka rasu bayan da wani jirgin sama ya fada kan wasu gidaje a garin Goma da ke gabashin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo, mintuna kadan bayan tashinsa.

Daga cikin wadanda suka rasu har da mutum hudu da jirgin ya fada a kan gidansu.

Gwamnan Arewacin Kibu, Mista Nzanzu Kasibita ya ce karamin jirgin ya tokari kasa ne a Unguwar Mapendo, bayan ya gaza tashi yadda ya kamata da safiyar Lahadi.

Hukumomi sun ce jirgin na dauke ne da fasinjoji 17 da ma’aikata biyu.

Ana yawan samun hadurran jirgin sama a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo saboda rashin bin ka’idojin kariya da rashin kula da lafiyar jirage, tuni aka haramta wa dukkan jiragen saman kasar yin balaguro zuwa kasashen Tarayyar Turai.

Wata majiya a filin jirgin saman garin Goma ta shaida wa BBC cewa jirgin mai suna Dornier-228 twin-turboprop, mallakin wani kamfanin sufurin jiragen sama ne a kasar da ake kira Busy Bee.

Jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa garin Beni, mai nisan kilomita 350 daga Goma.

Wakilin BBC ya ce ba a riga an tantance abin da ya haifar da hadarin ba, sai dai wata majiyar ta ce jirgin ya samu matsalar inji ne jim kadan bayan tashinsa.

Babu tabbas kan yawan mutanen da ke cikin gidajen da jirgin ya fada a kansu