✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya ci dangin ango 9 a Nasarawa

Wani biki ya juye bakin ciki, bayan da  motar da ke dauke da ’yan uwan ango su 13 suka gamu da hadari a makon jiya,…

Wani biki ya juye bakin ciki, bayan da  motar da ke dauke da ’yan uwan ango su 13 suka gamu da hadari a makon jiya, inda mutum tara daga cikinsu suka rasu uku suka jikkata. Hadarin ya auku ne bayan da daya daga cikin tayoyin motar kirar bas da ke dauke da su ta zare a kan hanyar Keffi zuwa Nasarawa, a kan hanyarsu ta zuwa daurin auren.

Wadansu da ke da nasaba da lamarin sun shaida wa Aminiya cewa mamatan wadanda gaba dayansu dangin ango ne, sun fito ne daga garin Talata-Mafara da ke Jihar Zamfara ne da nufin halartar daurin auren dan uwansu mai suna Babangida Tahir da kuma wata ’ya ga Sanata Abubakar Sodangi mai suna Fa’izah.

Daya daga cikin wadanda suka zanta da wakilinmu, ya ce sun iso Abuja a ranar Juma’a da dare, inda suka kwana sannan da gari ya waye suka kama hanyar zuwa wajen daurin auren wanda aka tsara yi da misalin karfe 11 na ranar Asabar.

Ya ce ango da wadansu abokansa suna cikin wata mota daban, lokacin da motar da ta yi hadarin wadda ke dauke da ’yan uwansa ciki har da waliyyi mai karbar auren suka gamu da hadarin da misalin karfe 10 na safe a wani waje da bai wuce kilomita 5 da shiga garin Nassarawa ba.

Ya ce jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) sun kwashe gawarwakin daga cikin motar wadda ya ce ta yi rugu-rugu, zuwa babban asibitin garin inda aka fara duba wadanda suka tsira da rai, sannan aka yi jana’izar mamatan a yammacin ranar. Ya ce mutum 3 ciki har da direban motar sun tsira da raunuka, inda daga bisani aka wuce da su zuwa Zamfara inda za a yi wa biyu daga cikinsu dorin gargajiya. Ya ce shi kuma direban motar an kai shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau.

Mutum daya ya tsira ba tare da ko kwarzane a jikinsa ba.

Wani dan uwan Sanatan da ya zanta da Aminiya, ya ce an daura auren da misalin karfe 12 na ranar bayan Mai martaba Sarkin Nasarawa ya ba da umarni ga babban limamin garin ya kasance a matsayin waliyyi saboda  wanda aka wakilta na cikin wadanda suka rasu.

Ya ce sun kai ziyarar gaisuwar ta’aziya garin Talata-Mafara tare da ango da Amarya.

A zantawarsa da Aminiya Sanata Abubakar Sodangi ya danganta lamarin da ikon Allah, inda ya yi wa mamatan fatar shahada. Sanata Sodangi ya ce daukacin mamatan kakansu daya ne.