✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya ci mutum 6, ya raunata 10 a Gombe

A safiyar Talatar da ta gabata ce wata babbar mota dauke da bandiran kwanon rufi ta yi hadari inda a sanadiyar haka mutum 6 suka…

A safiyar Talatar da ta gabata ce wata babbar mota dauke da bandiran kwanon rufi ta yi hadari inda a sanadiyar haka mutum 6 suka rasu 10 suka jikkata a kan gadar babbar hanyar garin Gombe.

Motar tana tafiya ne sai birki ya tsinke, inda ta yi gaba-da-gaba da wata babbar bas sannan nan take ta kama da wuta, ta kuma bankade masu Keke NAPEP uku da wadansu ’yan babura sannan ta fada kasar gadar.

Hadarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar.

A bana  sau uku ke nan ana samun irin wannan hadari na manyan motoci da suka hada da tankar mai da suke hallaka rayuka da dama da dukiyoyi.

Wani da hadarin ya faru kan idonsa ya ce motar ta taho ne daga Mil Uku za ta wuce hanyar Biu sai birki ya tsinke, inda aka yi ihu domin ankarar da mutane halin da ake ciki, wanda hakan ya sa mutane suka gudu, “Da mutuwar za ta fi haka,” inji shi.

Kakakin Hukumar Kare Hadura ta Kasa (FRSC), DRC Ibrahim Hassan Mustapha ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, mutum shida sun rasu goma kuma suka ji mummunan raunuka.