Da Dumi Dumi

Hadarin mota ya kashe mutum 12 a Neja

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC ) ta ce, mutum 12 ne suka mutu sanadiyyar hadarin mota yau Juma’a a kauyen Gwacipe da ke Karamar Hukumar Gurara ta jihar Neja.

Kwamandan Shiyya na Hukumar FRSC Mr Joel Dagwa, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai NAN yau a Minna babban birnin jihar Neja. Hadarin ya faru ne tsakanin mota tirela kirar DAF mai lamba KMW 08 AX da motar bas kirar Toyota Hiace mai lamba SSU 08 XA.

Hadarin ya rutsa da fasinjoji 25 yayin da 12 suka mutu, 9 daga ciki sun samu mummunan raunuka a yanzu haka suna babban asibitin tarayya da ke garin Gawu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya