✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe mutum 13 da raunata 11 a Nasarawa

Rahotanni na bayyana cewa, mutum 13 sun mutu sanadiyyar hadarin mota, yayin da mutum 11 suka samu raunuka a kusa da Unguwan Ciyawa a Karamar…

Rahotanni na bayyana cewa, mutum 13 sun mutu sanadiyyar hadarin mota, yayin da mutum 11 suka samu raunuka a kusa da Unguwan Ciyawa a Karamar Hukumar Eggon da ke jihar Nasarawa.

Kwamandan Hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC na Nasarawa Ismaila Kugu, ya bayyana wa majiyar mu cewa, cikin wadanda hadarin ya rutsa da su akwai matasa 10 da yara 3.

Ismaila, ya kara da cewa mutum 11 ne suka samu raunuka sanadiyyar afkuwar hadarin.

A yanzu haka an kai wadanda suka jikkata da gawarwakin zuwa asibitin Nasarawa Eggon.