✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe mutum 2 da raunata 8 a Ogun

An tabbatar da rasuwar mutum biyu a hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun jiya Sallah sanadiyyar hadarin mota. Kwamandan Sashe na Hukumar kare afkuwar…

An tabbatar da rasuwar mutum biyu a hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun jiya Sallah sanadiyyar hadarin mota. Kwamandan Sashe na Hukumar kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC na Ogun Mista Clement Oladele, ne ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai NAN hakan a Abeokuta babban birnin jihar Ogun a yau Laraba.

Mista Clement, ya ce hadarin farko ya faru ne da misalin karfe 4:52 na asuba a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a kusa da gidan man fetur na AP a garin Shagamu. Ya kuma ce, hadarin ya faru ne tsakanin tirela mai lamba KTU 565 XW inda ta kauce hanya ta yi sanadiyyar aukuwar hadarin.