✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe mutum 6 a Ogun

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum shida a wani mummunan hadari da ya faru tsakanin wata babbar mota da wasu motoci biyu kirar bas…

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutum shida a wani mummunan hadari da ya faru tsakanin wata babbar mota da wasu motoci biyu kirar bas a yankin J4 Ogbere a hanyar Shagamu zuwa Benin.

Babbar motar dai ta kauce wa hanyar da take bi ne wanda hakan ya yi sanadiyyar hadarin.

Kakakin hukumar bayar da agajin motoci a yankin Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da aukuwar lamarin.