✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe Mutum 7 a Jigawa

Mutum 7 sun mutu tare jikkata wasu mutum tara sanadiyyar hadarin da ya rutsa da wasu motoci biyu a Karamar Hukumar Maigatari da ke Jihar…

Mutum 7 sun mutu tare jikkata wasu mutum tara sanadiyyar hadarin da ya rutsa da wasu motoci biyu a Karamar Hukumar Maigatari da ke Jihar Jigawa.

Motocin da suka yi hadarin sun hada da, karamar mota kirar Peugeot 206 mai lamba TRN 948 AE da motar Golf 3 mai lamba FW 94 ABJ wanda ta taso daga kauyen Kwalande.

Majiyar mu ta samu rahoton yau Litinin, a yanzu haka wadanda suka jikkata suna babban asibitin Gumel, don yin jinya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Audu Jinjir, ya tabbatar da aukuwar hadarin.