Da Dumi Dumi

Hadarin mota ya kashe ‘yan Kwankwasiyya uku

Tambarin Kwankwasiyya

Wasu mambobin Kwankwasiyya uku sun rasu, yayin da biyu suka samu mummunan rauni a wani hadarin mota da ya faru a hanyar Kaduna zuwa Abuja jiya Litinin.

Hadarin ya faru lokacin da mambobin Kwankwasiyyar ke hanyar su ta zuwa Abuja don halartar zaman kotun koli wanda zata yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na APC da dan takarar PDP Abba Kabir Yusuf, da aka yi a shekarar 2019.

Kakakin dan takarar Gwamnan Kano a PDP Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya fitar da sanarwar.

Wadanda suka rasu sun hada da: Faisal Dabo, Abba Farouk Shehe da Hassan Sauna, wadanda suka samu rauni kuma su ne: Yahaya Muhammad da Imam, a yanzu haka ana ci gaba da jinyar su asibiti.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya