✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin tirela ya kashe mutum 6 da raunata 10 a Gombe

A kalla mutum shida aka tabbatar da rasuwar su yayin da wasu goma suka jikkata a wani hadarin babbar mota tirela da ta yi da…

A kalla mutum shida aka tabbatar da rasuwar su yayin da wasu goma suka jikkata a wani hadarin babbar mota tirela da ta yi da wata motar bas da kuma wasu babura mai kafa uku (Kake Napep) su uku a yau Talata yankin Kudancin jihar Gombe.

Majiyar mu ta gano cewa, hadarin ya faru ne sanadiyyar rashin birkin motar tirelar, wanda ya haddasa kaucewar motar zuwa afkawa motor bas da take dauke da fasinjoji da babura mai kafa uku, hakan ya haddasa rasuwar mutum shida nan ta ke tare da raunata wasu.

Daya daga cikin direbobin babur mai kafa uku mai suna Mukhtar, wanda ya tsallake rijiya da baya a hadarin da faru, ya ce tirelar bayan ta ture motar bas da baburan duk sun fada kasan gadar da take hanyar.

Hadarin ya faru ne a babbar hanyar yankin Hammadu Kafi cikin birnin jihar ta Gombe.