✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadin goge fata

Kowace mace ta cancanci kula da fatarta da kuma fuskarta. Domin mace aka fi sani da kwalliya da ado.Kasancewar irin aikace-aikacen gida, kamar su shara…

Kowace mace ta cancanci kula da fatarta da kuma fuskarta. Domin mace aka fi sani da kwalliya da ado.Kasancewar irin aikace-aikacen gida, kamar su shara da wanke-wanke da sauransu hakan na sanya fata dauda idan ba a kula wajen magance ta ba tana haifar da fesowar kuraje, kunar rana, gishirin fuska da maikon fuska.

Domin gyaran fata da jiki, dole ne a zabi daya daga cikin wadannan ababen da zan lissafo a goge fata a duk lokacin da aka yi wasu aikace-aikace a gida bayan an yi wanka. A sha karatu lafiya.

  • Idan ana da hali za a iya yin wanka da ruwan madara; domin madara na dauke da sinadaran sanya laushin fata da sanya ta sulbi.
  • Zuma; yawan amfani da zuma na rage gautsin fata kuma ya sanya ta laushi a kullum.
  • Ruwan kwai; yana hana fuskar zama a bushe kuma yana hana fitar gishirin fuska a fuska
  • Lemun tsami; yana hana kuraje fitowa kuma yana kara hasken fata.

Hadi  

Cokali daya na zuma

Cokali daya na madara

Rabin cokalin ruwan kwai

Ruwan lemun tsami kadan

Ki samu kwalba a hada ruwan madara da zuma sannan a dora a kan wuta na tsawon minti goma domin su hadu. Bayan haka, sai a zuba ruwan kwai da ruwan lemun tsami a cikin hadin sai a gauraya su sosai.

A samu auduga a rika shafawa da ita a fuska musamman gefen hanci. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti ashirin da biyar kafin a wanke.

A wanke fuska da ruwan dumi sannan a goge ta da tawul mai kyau.

Idan har a ka kasance masu yin irin wannan hadin, insha Allahu, za a rabu da kurajen fuska.