✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Hadin kai a kan gaskiya ginshiki ne na karfafa al’umma’

Hadin kai a kan gaskiya babban ginshiki ne na karfafa al’umma, musamman idan aka yi la’akari da karantarwar da addinin Musulunci ya yi a kan…

Hadin kai a kan gaskiya babban ginshiki ne na karfafa al’umma, musamman idan aka yi la’akari da karantarwar da addinin Musulunci ya yi a kan haka.
Wani malamin Musulunci, Assheikh Bashir Suleiman  ne ya fadi haka sa’ilin da ya gabatar da makala mai taken “Mahimmancin Hadin kan musulmi a kan gaskiya”, a taron wa’azin da kwamitin wa’azin  matasa na kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunna ta kasa reshen Jihar Kuros Riba da ke Kalaba ya shirya aka gudanar a harabar masallacin da ke kan titin Mary Slessor.
Ya ce halin ’yan uwantaka ta Musulunci abu ne muhimmi da yake sanya kaunar juna, kuma ya haifar da hadin kai, matukar aka gudanar da shi a kan gaskiya.
Malamin ya bayyana  bukatar kowane musulmi ya hada kansa da dan uwansa a kan turba ta gaskiya, wanda yin haka zai sanya al’umma ta zauna lafiya cikin jin dadi da walwala, lamarin da yake kai bawa kara kusantuwa zuwa ga Mahaliccinsa.
Assheikh Bashir ya ce matukar ana son  hadin kan juna, to kuwa wajibi ne a rika yi wa juna wasiyya da yin  hakuri da kuma kamanta  gaskiya. “Idan ba ma yi wa juna wasiyya da  gaskiya da rika yin hakuri da juna,  to hadin kanmu ba zai  yiwu ba. Haka ma  idan ana saba wa Mahalicci, ana yin shiru a yi biris da lamarin to, babu shakka za a samu cikas a fuskoki da dama na rayuwa”. Inji shi.
Malamin ya ce wani sinadarin da yake haifar da kyakkyawar kaunar juna shi ne  musulmi su rika yi wa juna sallama mai manufa ta gaskiya da kuma sadar da zumunci a kowane lokaci.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a dandalin wa’azin, babban limamin masallacin Izala da ke Kalaba, Assheikh Bashir Salihu Abuga ya yaba wa yunkurin da matasan ke yi dangane da irin wannan aiki na alheri.
Haka nan ya jinjina wa al’ummar musulmi da kodayaushe suke bayar da gudunmawarsu domin daukaka addinin Allah. Sai kuma ya jawo hankalin kowane musulmi ya kasance mai jin tsoron Allah a duk inda ya kasance.