✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadin kan Najeriya ne babban burina – Dakta Suwaiba Umar

Tarihinta: Sunana Suwaiba Umar Dodo Maradun, malama a Kwalejin Fasaha da kere-kere ta Ummaru Ali Shinkafi dake nan Sakkwato, ina bangaren koyar da turanci. Ni…

Tarihinta:

Sunana Suwaiba Umar Dodo Maradun, malama a Kwalejin Fasaha da kere-kere ta Ummaru Ali Shinkafi dake nan Sakkwato, ina bangaren koyar da turanci. Ni ‘yar asalin Maradun ce a Jihar Zamfara  kakana a lokacin shi ne Katuka kuma Magajin Maradun, diyan shi ba wanda ya gaje shi sai daga baya babban yayanmu ya karbi sarautar Katuka, sai muka dawo da zama Maradun, a lokacin Sakkwato da Zamfara suna hade. Mahaifina ya ba da gudunmuwarsa a Sakkwato matuka, ya zauna a garin Gwadabawa inda na yi karatun Firamare a makarantar cikin gari, da na kare sai aka sanya ni Sakandare ta Unity dake Illela.

Bayan na kammala sai aka min aure, sai muka tafi Ingila tare da mai gidana muka zauna, daga nan sai na fara karatu a can, daga baya na ga ba zan iya cudanya da mutanen na can ba, sai na dakatar da karatun,  da na dawo Najeriya sai na fahimci na yi wauta don zai fi sauki fiye da nan, bayan na gyara takardu na ne na shiga Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari inda ya samu takardar shaidar NCE, ina karewa sai na cigaba da yin digiri bayan kammalawa, sai na tura takardun neman aiki a wurarare da dama aka dauke ni a makaratar haddar Alkur’ani da Ilmin Islama ta Sarkin Musulmi Maccido, bayan nan na sayi fom na digiri na biyu na yi canjin aiki na dawo makarantar da nake yanzu daga nan ne shugaban makaratar ya kara mana kwarin gwiwa sai na koma na yi digiri na uku a Jami’ar Amurka na kare, a halin yanzu ni Dakta ce.

Kalubalen da ta fuskanta a rayuwa:

Alal-hakika babu wani kalubale ga abin da ka sanya wa rayuwarka cewa ka yarda zaka yi, don komai baya samuwa da sauki, na ga wasu suna wahala kafin su samu, amma ni bana kula da wani kalubale, na rigaya na aza rayuwata sai na yi karatu, mafi yawan cikas da wasu ke samu ba su shiryawa karatun ba ne, kuma ba Allah ne ke sanya wa gaba ba, a gidanmu duk wacce ta gama sakandare ba ta ci gaban karatu sai bayan aurenta, idan mijinta ya so ya bar ta ta ci gaba. To Alhamdulillahi ni mai gidana ya bani goyon baya sosai, dalilin kenan da nake jin ban samu cikas ba.

Ko burinta na kuruciya ya cika:

Burina shi ne ina son Najeriyar nan a samu hadin kai, ta yadda za a ajiye kabilanci gefe guda don samun cigaba, haka Indiyawa da Japanawa da Rashawa suka yi, suka samu cigaba, amma mu abin da ke takura mana ke nan a kasar nan, kabilanci da addini, shi ya sanya muka tarwatse komai ya ja baya ga harkar tsaro da tattalin arziki, hadin kai a Najeriya ne burina tun ina karama.

Abin da take so a rika tuna ta da shi:

Babbar magana, wani lokacin kana yin abu ne amma ba ka san za a tuna ka da shi ba, ina son mutane su sani ina da tausayi idan mutum yana neman abu gare ni ko zai cuce ni ban ce masa a’a, wani lokaci ma nakan yi wa wasu addu’a ban yi wa kaina ba, ina taimakon mata da marayu, wadannan da wasu halaye nawa sukan sanya kila mutane su tana dani, domin kana yi wasu na kallon kamar kai siyasa ce kawai kake yi ko neman suna, amma ni da kaina ban san wani abu da mutane za su tuna da ni ba kila ko karantarwa da nake yi wallahu a’alam.

Abin da ya faru wanda ba za ta taba mantawa ba:

Abin da ya tsaya min a rai a lokacin bai fi ina makarantar sakandare mahaifiyata ta yi rashin lafiya, aka kirani aka ce na dawo gida, hankalina ya tsahi sosai saboda bani da kamar ta, tana dawainiya da ni matuka, da na zo gida na samu an yi mata aiki a asibiti, inda na zauna tare da ita har aka sallameta ta dawo gida. Ba ni manta wannan, ya tsaya min a rai duk da har yanzu na yi sa’a muna tare da ita a raye, mahaifina ne ya rasu, shi kadai ne ya tsaya min, domin mu danginmu daya ne, muna tare komai muna farin ciki da bakin ciki tare, mun yarda da kaddara.

Tarbiyar mata matasa a yanzu:

Idan akwai wadda ya kamata ya samu tarbiyya da kula na musamman, to ‘ya mace ce, kuma iyaye ya kamata su yi wannan dawainiya, saboda tarbiyyar mace ta al’umma ce, akwai matsala ga wasu sai dai iyaye su roki Allah Ya shirya su, don ‘yan matan yanzu baka ma san abin da suke so ba, ba sanin ciwon kai ko abin da suke so ba, wanda Allah ke aza masu daban sun kasa tsayar da kansu su zabi rayuwa mafi inganci, idan aure suke so su je su yi, idan karatu ne su tsaya kanta, amma ka gansu ba ka ma san ta in da zaka soma ba, duk abin da zan yi in ga mata ina son na fara da su saboda muna da rauni wallahi, suna ba ni tausayi sun warwatse ba su san abin da suke so ba. Abin da nake ganin ya jawon wannan ci bayan rashin tawakkali da dogaro da kai ne, sannan tarbiyyar daga iyaye ta sukurkuce, kwadayi ya dabaibayi yaran da iyayen, abin yana daure min kai, don ba haka uwayenmu suka yi mana tarbiyya ba, ka ga mace na tafiya tana shan rake ko agwalima ko gyada a kan hanya, ko namiji ka gani yana cin abu a hanya ka san ba shi da tarbiyya ballantana mace, ya kamata al’umma ta tashi tsaye ko za a iya samun gyaran wannan lamarin.

Ko ta gamsu da yanda mata ke tafiya makaranta?:

Na gamsu amma to yawan matan a makaranta suna karatun ne ko suna zuwa ne don kwalliya, sai a duba don wasu matan ba su karatu ka duba sakamakon yarinya ba ta ci komai ba cikin kashi 100 nasu 20 ne kawai ke karatu. Shawara ta ga mata ita ce, su san ciwon kansu in sun yi aure su rike amanar yaransu su tarbiyyatar da su, su yi ilmi don diyansu su yi kwaikwayo da ita, ga diyana nan sun ce min da ni suke kwaikwayo suna son su yi ilmi fiye da ni, duk in da mace take ta sani ba wani abu da za ta yi bai komawa ‘ya’yanta ba, ko mai kyau ko akasinsa, don haka mu ji tsoron Allah a dukkan lamarinmu.

Ko burinta na rayuwa ya cika?:

Na gode Allah na yi karatu ana kirana Dakta, abin da ban zanci zan kai ba. Ko anan ilmin ya tsaya na cika burina na rayuwata. Ba na kwaikwayon wata kishin yadda ake kiran wasu a gabana sun ci kyauta ne a makaranta da yadda mahaifiyata ke wahala ta ga dai mun yi karatu, ya sanya ni jajircewa na ga sai na cika mata burinta.

Iyalanta:

Ina da ‘ya’ya takwas, mata hudu maza hudu. Babbar ita ce Zainab sai Khadija sai Hassan da Hussaini sai Abba sai kuma Amina sai Auwal sannan da kuma Rukayya ‘yar auta.

kasashen da ta ziyarta:

Na tafi Nijar da Ghana da Afirka ta Kudu da Dubai da Ingila can na fi dadewa na tafi Amurka da Saudiyya. Ina son in tafi Chana da Faris da kuma Masar.