Da Dumi Dumi

Haduwar Hanya: Fim din da kare ke cikin manyan jarumai

A wani fim da ba a saba ganin irinsa ba a Kannywood, Jarumi Zahraddeen Sani, wanda aka fi sani da Owner ya dauki nauyin shiryawa, zai kasance na daban a tarihin Kannywood.

Fim din mai suna Haduwar Hanya, kare zai kasance cikin manyan jarumansa, kuma akwai manyan jaruman da za su taka rawa a cikinsa.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Premium Times, Zahraddeen Sani ya ce a kullum burinsa ya kawo wani sauyi a Masana’antar Kannywood.

“Na yi shekaru ina shirya wa wannan fim din. Na kalli fina-finai da aka yi irin wannan tsari, amma na san tsari ne kawai. Amma ina son nawa ya kasance na gaskiya, kuma da Hausa. Daga Spain na sayo karen, inda na kashe dubban daloli.

“Sai na kawo shi nan gida na fara koya masa abin da nake so. Na koya masa Hausa. Zan iya masa magana da Hausa kuma ya yi abin da na umarce sh,.” inji shi.

ADVERTISEMENT

Shi dai fim din na Haduwar Hanya an shirya shi ne kan yadda wadansu suke amfani da sunan soyayya su fallasa wani abin sirrin wadansu.

A cikin fim din akwai jarumai irin su Ali Nuhu da Rahama Sadau da Nafisat Abdullahi da Uzee Usman da Abdul M. Shareef da Rabi’u Rikadawa da sauransu.

An fara daukar fim din ne a ranar Talata da ta gabata.

Zahraddeen Sani ne ya dauki nauyin fim din, sannan Ali D Man da Mu’azzam Idris suka shirya, Jamilu Nafseen ya tsara labarin.

Yunusa Mu’azu ne Mataimakin Darakta, sai Alfa Zazee Muhammed ya bada umarni.

Da take bayani kan fostar fim din a shafinta na Instagram, Jaruma Rahama Sadau ta ce, “Kaiiii! Har da kare?” shi kuma Zahraddeen Sani ya ce, “Wallahi. Kuma rawa mai kyau zai taka!”

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya