✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haduwar Hanya: Fim din Hausa da kare ke cikin manyan jarumai

A wani irin fim da ba a saba ganin irinsa ba a Kannywood, jarumi Zahradden Sani, wanda aka fi sani da owner ya dauki nauyin…

A wani irin fim da ba a saba ganin irinsa ba a Kannywood, jarumi Zahradden Sani, wanda aka fi sani da owner ya dauki nauyin shirya wani fim wanda salonsa zai kasance na daban a tarihin Kannywood.

Fim din mai suna Haduwar Hanya, kare zai kasance cikin manyan jaruman fim din, duk kuwa da cewa akwai manyan jaruman da za su taka rawa a cikinsa.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Premium Times, Zahraddeen Sani ya ce shi kullum burinsa ya kawo wani sabo da ba a saba gani ba a masana’antar Kannywood.

“Na yi shekaru ina shirya wa wannan fim din. Na kalli fina-finai da aka yi irin wannan tsarin, amma na san tsari ne kawai. Amma ina son nawa ya kasance na gaskiya, kuma da Hausa. Daga Spain na sayo karen, inda na kashe dubban daloli.

“Sai na kawo shi nan gida na fara koya masa abin da nake so. Na koya masa Hausa. Zan iya masa magana da Hausa kuma ya yi abin da umarce shi.”

Shi dai wannan fim din na Haduwar Hanya an shirya ne kan yadda wasu suke amfani da sunan soyayya wajen yaudara, sannan su fallasa wani abun sirrinsu.

A cikin fim din akwai jarumai irinsu Ali Nuhu da Rahama Sadau da Nafisat Abdullahi da Uzee Usman da Abdul M. Shareef da Rabiu Rikadawa da sauransu.

An fara daukar fim din a yau, Talata 17 ga Maris.

Zahraddeen Sani ne ya dauki nauyin fim din, sannan Ali D Man da Mu’azzam Idiri suka shirya fim xin Jamilu Nafseen ya tsara labarin.

Yunusa Mu’azu ne mataimakin darakta, sannan Alfa Zazee Muhammed ya bada umarni.

Da take mayar da martani kan fostar fim din a kwanakin, jaruma Rahama Sadau cewa ta yi, “Kaiiii! har da kare?” inda shi kuma Zahraddeen Sani ya ce, “Wallahi. Rawa mai kyau zai taka. Kma saboda fim xin nan na kuma atisaye sosai.”