✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haduwar Idin Babbar Sallah da bikin Yahudawa ya jawo tankiya a Masallacin Kudus

Haduwar Idin Babbar Sallah da wani bikin Yahudawa ya jawo’ yan sandan kasar Isra’ila, sun harba hayaki mai sa hawaye tare da yin amfani da…

Haduwar Idin Babbar Sallah da wani bikin Yahudawa ya jawo’ yan sandan kasar Isra’ila, sun harba hayaki mai sa hawaye tare da yin amfani da harsashin roba da jefa gurneti don tarwatsa Falasdinawan da suke ibada a Masallacin Al-Aksa da ke gabashin birnin Kudus.

Dubban Falasdinawa ne suka taru a ranar Lahadi, a masallacin, rana ta farko ta bukukuwan Babbar Sallah.

Sai dai ranar ta ci karo da ranar hutun Yahudawa da suke wa take da Tisha B’Ab, wanda rana ce da Yahudawan ke kara tudada zuwa wannan guri mai daraja a addinan biyu.

Dubban Falasdinawa ne suka taru a harabobin shiga wurin; bayan samun rahoton cewa, ‘yan sandan za su kyale Yahudawa masu ziyarar su shiga cikin masallacin.

A yayin da suke dauki-ba-dadi da ’yan sandan Isra’ila a wuri na uku mafiya daraja a addinin Musulunci, an jiyo Falasdinawan suna furta kalaman: “Da rayukanmu da jininmu, sai mun ceto ka, Masallacin Aksa!”

Kungiyar Agaji ta Red Crescent, ta ba da rahoton cewa an raunata Falasdinawa 61; yayin da aka garzaya da 15 cikinsu, zuwa asibiti.

Karkashin wata dadaddiyar yarjejeniya a tsakanin mahukuntan Musulmin da na Yahudawa, an haramta wa Yahudawan yin ibada a wurin.

Sai dai a shekarun baya bayan nan, masu tsaurin addinin Yahudu sun zafafa kai ziyara wurin, a wani abin da ake kallon, yunkurin yin karan-tsaye ga wancan tsohuwar yarjejeniyar ce; yayin da Falasdinawa ke kallon lamarin a zaman takalar fada, kuma suke fargabar Isra’ila na take-taken kwace wurin.

Isra’ila dai na daukar dukkan birnin Kudus a zaman babban birninta; yayin da Falasdinawa ke son yankin birnin da aka mamaye, ya zama babban birnin kasarsu, a nan gaba.

Wani wakilin tashar talabijin ta Aljazeera, mai aiko da rahotanni daga birnin Kudus, Harry Fawcett, ya ce zaman tankiya na kara ruruwa a yankin, cikin ’yan kwanakin nan.

“An bude kofar shiga wurin, amma an kyale wadanda ba Musulmi ba, sun kutsa ciki. An samu fito-na-fito; sai kawai muka ga ’yan sanda sun kutsa domin tarwatsa jama’a,” inji wakilin Aljazeera.

“A lokacin ne kuma muka ga ’yan sanda na amfani da harsasan roba da hayaki mai sa kwalla tare da amfani da gurneti. Akwai wani yunkuri mai karfi daga gwamnatin Isra’ilar domin samun damar kutsawa wannan wuri da zimmar nan gaba a fara gudanar da ibadar Yahudawa a ciki, kuma wannan ka iya zama silar wannan fito-na- fito,”inji Fawcett.

‘Masallacinmu ne’

Bayan samun lafawar al’amura wanda ya zo bayan kakkausar suka daga ’yan siyasar Isra’ila; ’yan sandan sun bude wurin ga Yahudawa masu ziyarar; wanda hakan ya kara rura wutar rikicin.

“Masallacinmu ne, kuma Idinmu ne,” inji wata mata mai suna Assisa Sneinah ’yar shekara 32, ta ce tana wajen a lokacin da rikicin ya barke.

“Kan ka ce kwabo, sai muka ga jami’an tsaro sun yi wa wurin tsinke tare da harba gurnet-gurneti,” inji matar.

Yahudawan da yawansu ya kai 1,300 ne suka ziyarci wurin a ranar Lahadi, kamar yadda wata Kungiyar Musulmi mai suna Wakf, wacce take kula da masallacin ta shaida.

Ali Abunimah, wanda ya assasa gwagwarmayar  Intifida na zamani, ya gaya wa Aljazeera cewa, idan  da Isra’ilar ta so, to kuwa da an kauce wa faruwar yamutsin, ta hanyar hana masu kaifin kishin addinin Yahudu, karkashin Kungiyar Temple Mobement kai ziyara wannan wuri; musamman a ranar da Falasdinawa ke shagulgulan Babbar Sallah.

Abunimah, ya ci gaba da cewa, “A ranakun ibadar Yahudawan, Isra’ilar takan rufe dukkan hanyoyin yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza, wanda hakan ke hana miliyoyin Falasdinawa ’yancin watayawa tare da damar shiga birnin Kudus, ko kuma ma damarsu ta ziyartar wurare masu tsarki a gare su, kawai domin a bai wa Yahudawan damar gudanar da ibadarsu cikin tsanaki,” inji shi.

“Amma sai a Ranar Idin Babbar Sallah, Isra’ila ta yi wani abu na daban, ta kyale masu kaifin kishin Yahudanci suka kai ziyara zuwa masallacin na Al-Aksa da nufin tunzura al’ummar Musulmi. Kuma ina ga abu ne a fili cewa wadannan Yahudawa ba na kwarai ba ne da suke ziyartar masallacin domin ibada,” inji shi.

“Wannan tsararren abu ne kawai, da ’yan Kungiyar Temple Mobement na Yahudawan suka kitsa don ta-da-zaune-tsaye. Kuma ita kungiya ce da ke samun tallafin kudi daga gwamnatin Isra’ila, wadda babban muradinta shi ne ta rugaza masallacin Al-Aksa tare da mayar da shi wurin bautar Yahudawa,” inji shi.

‘Yunkurin takalar fada ne kawai

Kasar Jordan, wacce take kula da masallacin, kuma kasar Larabawa ta biyu da take da yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila, ta yi tir da matakin na Isra’ilar na ci gaba da yi wa yarjeniyoyin da aka kulla karan-tsaye.

Hanna Ashrawi, wata jigo a kungiyar kwato hakkin al’ummar Falasdinawa (PLO), ta zargi Isra’ila da neman rura wutar rikicin addini da na siyasa a yankin.

Ta fadi a cikin wani sakonta cewa: “Dirar wa Masallacin Al-Aksa da dakarun mamaya na Isra’ila suka yi a safiyar ranar Idi, wani yunkuri ne na neman ta-da-zaune- tsaye kawai, kuma na ganganci.”

Wannan wurin dai ya kasance ne a barayin gabashin birnin Kudus, wanda Isra’ila ta mamaye a wani yakin Gabas ta Tsakiya a 1967, a wani yunkurin da bai samu goyon bayan kasashen duniya ba.