✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Haduwarku ta son zuciya ce – Yerima Giyade

Alhaji Yerima Aliyu Giyade Ajiyan Giyade Giyade daya daga cikin dattawan Jihar Bauchi da ya rike mukaman kwamishina a jihar, kuma mamba a Majalisar Dattawa…

Alhaji Yerima Aliyu Giyade Ajiyan Giyade Giyade daya daga cikin dattawan Jihar Bauchi da ya rike mukaman kwamishina a jihar, kuma mamba a Majalisar Dattawa masu bayar da shawara ga Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya jagoranci wani ayari na dattawan da suka kunshi Barayan Bauchi Alhaji Sunusi Baban Takko zuwa Sakatariyar ’Yan jaridu ta Bauchi inda suka mai da martani ga su Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi game da hadewarsu da ’yan adawa don kada Gwamnan a zabe mai zuwa, ya amsa tambayoyin manema labarai ciki har da wakilinmu kamar haka:

 

Me ya kawo ku wajen manema Labarai?

Akwai wadansu da suka hadu suka ce sun hada kai domin su kada Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, kuma suka ce su masu ruwa-da-tsaki a al’amuran Jihar Bauchi, sai muka ga bai kamata ba a matsayinmu na masu ba shi shawara kuma masoyansa kuma muna da ta cewa a Jihar Bauchi a ce mun yi shiru ba. Muna shaida wa alummar Jihar Bauchi da duniya cewa wadancan mutane abin da suka fada ba daidai ba ne, sun fadi abu ne don son zuciyarsu. Misali sun hada jam’iyyu bakwai har da APC a ciki, abin da ya ba mu mamaki, shi ne me zai kawo dan APC ya yi tarayya da PRP da wasu jam’iyyu, shi dan APC wa zai kayar? Da shi ake fada amma kuma ya shiga cikinsu, wadannan mutane mun tabbata su ma a rabe suke kuma nan da kwana kadan za a ji su. Jiya-jiya daya daga cikin shugabanninsu ya fito fili, ya karyata abin da suka yi, ya ce ba za su iya fid da mutum daya ya wakilce su ba.

Ba mu muka fada ba daya daga cikin wadanda suka sa hannu a takardarsu ce ya fadi haka ga duniya cewa ba za su iya fid da mutum daya a cikinsu ya wakilce su a jam’iyya daya ba domin kowa aniyyar kansa yake yi, kawai yanzu ne wani mai sauri ya ja su a yi magana a hada kai don a yi bacel. Kuma na tabbata jama’ar Jihar Bauchi suna gani kuma duk sharrrin da suke yi har a ce Shugaban Kasa an yaudare shi ya daga hannun Gwamna. Shugaban Kasar ba a jawo shi da karfi ya daga hannun Gwamna ba, kuma mutanen da suka zo filin nan ba sayensu aka yi ba, ba biyansu aka yi ba, ba mutanen Filato ba ne, ba mutanen Gombe ba ne ba mutanen Yobe ba ne. Mutanen Bauchi ne kuma kowa don kansa ya zo ya tarbi Shugaba Buhari saboda kuma ya amince da Jam’iyyar APC da kuma Gwamnan APC. Da ba sa son Gwamnan mutanen Bauchi ko da Buhari kawai suke so, za su ce masa ka-tsaya a Abuja ba sai ka zo mana yakin neman zabe da kanka ba mun yafe. Amma Buhari ya zo Bauchi, mutanen Bauchi sun tare shi, tarba mai kyau ya daga hannun Gwamna ba wanda ya ce ba maso sai mutum 21 kawai a ce wai suna nuna kiyayya duk taron da aka yi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa a ce wai mutanen Bauchi ba su son Gwamna wannan ba gaskiya ba ne. Mutanen Bauchi suna tare da Gwamnan su.

Na biyu ina kira ga wadannan dattawa da sauran alummar Jihar Bauchi cewa, halin da muke ciki a jihohion Arewa maso Gabas har yanzu babu tabbataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali, ina rokon jama’a mu kiyaye harcenmu, saboda akwai makiyanmu a tsakaninmu, akwai wadanda suke so gaba daya in ba su ba a barar, to in an barar shekaru nawa ne suka rage mana? Wadanda muka haifa ’ya’ya da jikokinmu mece ce makomarsu? Ina kira gare su wadannan zazzafan kalamai da kausasa harce da suke yi wajen yakin neman zabe ko a wajen hira da ’yan jarida don Allah su yi su yi hakuri don sun wuce haka. Abin kunya ne ma inji mai hankali dattijo wanda ya rike matsayin a zo a gani a Najeriya, yana kalmomin batsa da kalmomin tashin hankali a gaban ’yan jarida to me ’ya’yansa da matansa da jikokinsa da masoyans za su ce? Ai ba daidai ba ne, ina kira gare su don Allah don Annabi su yi amfani da kalmomin da suka dace wadanda za su kawo zaman lafiya a Bauchi a yi zabe lafiya a gama lafiya, ba kalmomin da za su sa mutane su kara zafin kai a kan na musu zafin kai ba.

Gwamna ne ya turo ku ku kare shi?

Ni ina cikin Jam’iyyar APC, kuma abin da aka koya mini shi ne bin na gaba bin Allah, ba yadda zan yi in zagi wani babba a nan Bauchi wanda ya fi ni ko da wata daya ne bare Gwamna da ba ni kadai na zabe shi ba dubban mutane suka zabe shi a Bauchi. Mu muna taimakonsa ne saboda muna sonsa muna kaunarsa, mun kuma yarda da abin da yake yi, kamar yadda su ma suke fada suna son kansu ba su yarda da abin da yake yi ba kuma ba sa sonsa.

Amma sun ce sunayin wannan abu ne don kishin Jihar Bauchi?

Babu kishin Bauchi a ciki, idan kishin Jihar Bauchi ne na yarda Bello Kirfi shi kadai yana daya daga cikin mutanen da suka yi yaki muka samu Jihar Bauchi, amma wanda ya je APC ya yi takarar mukami a APC ya fadi zabe a APC kuma ya zo yana zagin APC kuma ya hada kansa da makiya APC mene ne kishin Bauchi? Kishin kansa ne ba kishin Bauchi ba.

Yanzu kun razana da wannan hadakar da suka yi ke nan?

Ba mu razana ba, idan mun razana ai sun yi taro a Bununu kun je kun gani, mun yi taro a filin wasa na Bauchi ba fa kaji ko tumaki muka tara ba mutane ne, me suka tara a Bununu ba su tara kaji ko awaki ba mutane ne, ta yaya za mu ji tsoron wannan? Babu abin tsoro ko kadan.

Wane kokari kuke yi don ganin Gwamna ya gyara kura-kuransa idan akwai?

To tunda Bature ya bar kasar nan Najeriya mun kare gyaran kura-kuranmu ne? Ai ba mu kare ba, muna kai za mu gyara,

Wadanda suka yi hadakar fa suna cikn wadanda suka tallafa masa ya zama Gwamna…?

Gyara kalmarka suna cikin wadanda suka yi tafiya tare da shi, su ma matsayi suke nema shi ma matsayi yake nema amma ba su dafa masa ba.

Amma sun goyi bayansa a zaben fid-da-gwani har ya zama Gwamna daga baya suka samu sabani?

Ka ce sun mara masa a zaben fid-da-gwani sun yarda ya fito takarar zaben fid-da-gwanin ke nan. In har suka mara masa suna sonsa suna kaunarsa sun yarda da shi ke nan to kuma me ya kawo fada?

Karon mulkinsa na farko muke magana?

Dakata ka ji ka taba jin aure a shekara guda a ce maka ba auren da ya mutu? Akwai auren da aka yi shi da niyyar zai mutu ba a taba yin aure don ya mutu ba, amma aure yana mutuwa.

Ko kuna da kwarin gwiwa cewa al’ummar Jihar Bauchi za su zabi Gwamnan ganin cewa ga ayyukan da ya faro bai karasa ba?

Tunda Bature ya bar kasar nan akwai ayyukan da ba a karasa su ba, ai ga dam din Mambila tunda Bature ya bar kasar nan ake kokarin yin sa amma sai yanzu ake yin aikin. Mutum komai kokarinsa komai kimarsa bai isa ya ce za mu yi maganin wahalhalun Jihar Bauchi a cikin shekara uku da rabi ba, wallahi ko shi wane ne ya zo ga ni ga shi.

A haka za a sake zabensa?

Ai zabensa kam insha Allahu an gama, abin da muke jira lokaci, jiya ya fita rangadi jiya ma haka kuma ko’ina goyon bayan jama’a ke ba shi da tabbacin zabensa.

Wannan dambarwa fa a cikin gidan Jam’iyyar APC ake fama da ita?

Me ya kashe Jam’iyyar PDP fadan cikin gida ni danta ne a da, fadanmu ne ya kashe ta yanzu kuma APC ta yi dadi, ta yi zaki ta yi karfi ita ce jam’iyya mai nasara ita ce mai cin zabe yaya ba za a yi fada ba? Kana so ina so.

Daga cikin abin da al’umma ke kokawa daminar da ta wuce an yi iska wadda ta lalata gine-gine an ba wa mutane gudunmawa Gwamnatin Tarayya ma ta ba da tallafi amma har yanzu Gwamna bai raba ba ko kwandala ba?

Ai ka san shi kadai ba zai yi ba, dole ya nada kwamiti wanda zai bi ya tattaro kudaden nan, wani kudin alkawari ne zuwa yake yi ba a gan shi ba. Amma an nada kwamiti insha Allahu cikin watan nan zuwa watan gobe mutane za su ga an fara aiki da wannan kudi, domin wadansu alkawuran sun cika amma har yanzu akwai wadanda suka yi alkawari amma kudin bai shiga hannu ba.