✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Azumi Muhammad: Burina mace ta zama gwamna a Jihar Taraba

Hajiya Azumi Muhammad  ta yi fice a gwagwarmayar siyasa a Jihar Taraba. Ita ce Shugabar mata ta tsohuwar jam’iyar ACN a Jihar Taraba, ta shiga…

Hajiya Azumi MuhammadHajiya Azumi Muhammad  ta yi fice a gwagwarmayar siyasa a Jihar Taraba. Ita ce Shugabar mata ta tsohuwar jam’iyar ACN a Jihar Taraba, ta shiga siyasa ne don ta taimaka wa mata, ba ta da wani aiki sai taimakon mata a birane da kauyuka.

Tarihin rayuwata
Assalamu Alaikum, Sunana Hajiya Azumi Muhammad, an haife ni a karamar Hukumar Lau da ke Jihar Taraba. Na yi Firamare a Lamkubari da ke Jihar Taraba, makarantar sakandare kuma a garin Numan da ke Jihar Adamawa. Bayan na kammala  sai aka yi mini aure. Amma abin takaici auren bai je ko’ina ba, sai na shiga Makarantar Fasaha da kere-kere ta Jihar Taraba da ke garin Wukari, bayan na kammala sai na ci gaba da karatu a Kwalejin Horar da Malamai ta Jalingo, inda na samu takardar shaidar malanta ta kasa (NCE). Daga nan na fara kasuwanci da siyasa. Tun ina karama nake son harkar taimakon mata ’yan uwana.
Gwagwarmayar rayuwa
Na sha gwagwarmaya a rayuwata, amma akwai wadanda ba zan iya mantawa da su ba, harkar kasuwanci da siyasa su ne kan gaba. A fagen siyasa na yi gwagwarmaya kasancewar tun da fara siyasa ta adawa nake yi, hakan ya sanya muka fuskanci matsaloli da dama kadan daga cikinsu, a shekarar 1999 da na nemi takarar kansila an yi wa rayuwata barazana, amma ban bayar da kai bori ya hau ba har sai da aka yi zabe aka kayar da ni. Da zabe ya sake dawowa sai na tsaya takarar majalisar jiha, nan ma ba a samu canji ba daga abin da ya faru a farko, daga nan na koma bangaren shugabancin jam’iya aka jijjiga aka rairaye cikinmu biyar da muka fito na samu nasara ta zama shugabar mata ta jam’iyar AC a Jihar Taraba, inda na rike wannan mukami har sau uku, daga nan na zama daraktar kungiyar fafutikar Janar Buhari har ya samu nasara a Jihar Taraba, a yanzu kuma ni ce shugabar mata a jam’iyar ACN, ba za mu daina gwagwarmaya ba sai gaskiya da adalci sun tsaya da kafafunsu a Jihar Taraba, ko kuma lokacin da rai ya yi halinsa. Na shiga siyasa a lokaci guda na yi wannan gwagwarmaya saboda mata su fita daga cikin kangin da suke ciki, ina tausaya wa mata sosai ba don ina mace ba, sai don haka ya dace. Harkar kasuwancina kuwa muna shan wahala ga masu sayen kayanmu ne.
Nasara
Na samu nasarori a rayuwata wadanda ba zan taba mantawa da su ba. Da farko na samu nasarar zama shugabar mata, na tsayar da dan takarar kansila wanda shi ma ya samu nasara, na tarbiyantar da ’ya’yana cikin addinin Musulunci, kuma ni da su muna cikin koshin lafiya tare da walwala.

Fatana
Ina yi wa ’yan uwana mata fatan alheri, ina kuma kira da mu hada kai a duk lokacin da wani abu da ya taso na harkokin rayuwa kamar addini da siyasa, idan mu mata mun hada kai duk abin da muka sanya a gaba za mu samu nasara, sabanin haka kuwa ci baya ne zai same mu, kamar yadda muke ta fama da shi a yanzu, ka dubi gefen siyasa mata da yawa ne ke fitowa neman wata kujera amma nawa ne suke samu saboda babu hadin kai. Ina kira ga mata mu yi hakuri, hakan ne zai iya kawo mana hadin kai ya kawar mana da matsalolinmu, don mu mata ba mu rabuwa da matsala, duk kuma dalilin rashin hadin kai. Mu kuma tsayar da gaskiya; mu aiwatar da maganar Bahaushe da yake cewa “ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne”. Mu cire son kai da son girma da neman ‘yar dangi a zuciyarmu, hakan ne zai kawo mana canjin da muke bukata musamman a nan Jihar Taraba da darajar mata ta yi kasa, duk wani abin kirki ba za ka gansu ba.
Ga mata matasa kuwa shawarar da zan ba su ita ce, a wannan lokacin da muke ciki na dimokuradiyya ana amfani da su fiye da kowa wurin cim ma burin siyasa daga baya a jefar da su, don haka su yi hattara, lokaci ne da kowa ya san abin da ke faruwa a kasar nan, ya kamata su natsu su yi abin da zai cece su ba abin da zai halaka su ba, rayuwa a yanzun nan akwai damuwa da yawa, sai ka ga mace na mayar da kanta kamar ita ba wata halitta ba ce ta Allah, ba wani nazari mai kyawu, a mayar da hankali ga samun kyakkyawar manufa.          
Burina a rayuwa
Gaskiya burin da nake da shi a rayuwa in Allah Ya sa na yi nisan kwana shi ne, ina son in zama wata abu a Jihar Taraba, mata duk inda suke su zama wani abu mu wuce zama kwamishina, ma’ana ba wai mukamin kwamishina kawai za mu rike ba, ina burin mace ta zama gwamna,wannan burina ne mace ta zama gwamna a Jihar Taraba.