Da Dumi Dumi

Hajiya Bilkisu Mainasara ta kwanta dama

Marigayiya Bilkisu Mainasara
Marigayiya Bilkisu Mainasara

Allah Ya yi wa Hajiya Bilkisu Mainasara rasuwa, a safiyar Lahadin da ta gabata da misalin karfe tara.

Marigayiyar, kafin rasuwarta, ta yi gajeruwar rashin lafiya bayan da ta gama Sallar Asuba a wannan rana.

Bilkisu, kafin rasuwarta, ma’aikaciya ce a Sashin Ilimi na Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina. Ta rasu tana da kimanin shekara 44. Ta bar mijinta, Alhaji Tanimu Yusuf Kaka na Hukumar Ilimin Bai-Daya (SUBEB) ta Jihar Katsina da ’ya’ya biyar, maza uku mata biyu da kuma ’yan uwa da dama. Allah Ya gafarta mata da rahama, amin.

Share