✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Bilkisu Yusuf: Babbar Katanga ta fadi

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, watau ranar babbar sallar , Allah Ya yi wa fitacciyar ‘yar jaridar nan Hajiya Bilkisu Yusuf rasuwar…

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, watau ranar babbar sallar , Allah Ya yi wa fitacciyar ‘yar jaridar nan Hajiya Bilkisu Yusuf rasuwar a sakamakon turmutsitsin da ya auku a wurin jifar Shedan da ke Muna a kasar Saudiyya a yayin gudanar aikin hajjin bana.

Hajiya Bilisu Yusuf Yusuf wacce mace ce mai kamar maza da ta yi fice a matsayinta na ‘yar jarida mai fafutikar ganin an gina kasa, ta tafi aikin hajjin bana a matsayin daya daga cikin jami’ai masu taimaka wa Alhazan Najeriya, ashe tafiyar tata ba na dawowa ba ne.
Duk wanda ya san Hajiya Bilkisu Yusuf zai ce mace mai himma da saukin kai da hakuri da juriya da son taimaka wa mai karamin karfi. Saboda haka ta taka rawa sosai wajen ganin an ganin Tarayyar kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) ta bude asibiti a Badarawa da ke garin Kaduna domin domin taimaka wa mata da yara da sauran mutane masu karamin karfi.
Majin Hajiya Bilkisu Yusuf wanda shahararren ma’aikacin banki ne wanda kuma yana daya daga cikin wadanda suka assasa bankin musulunci na Ja’iz, Alhaji Mustapha Muhammad Bintube, ya bayyana cewa, ‘Hajiya Bilkisu Yusuf ta rasu ne a yayin da take aikin Allah da kuma aikin gina kasa, domin mace ce mai kwazo kwarai, domin tana cikin wadanda hukumar Aikin Hajji ta kasa ( NAHCON) ta gayyata domin yin jagoranci yayin aikin hajji. Yadda na samu labarin rasuwarta shi ne, wata ‘yar uwarta da suke tare ta ce Hajiya Bilkisu Yusuf ta rasu ne a hannunta bayan da aka yi turmutsitsi a wurin zuwa jefar Shedan. Duk da cewa ina kaunarta, amma ina yi mata murna, don ta yi shahada, da fatan Allah ya jikanta, amin.’
dan marigayiyar Moshood Sanusi Yusuf shi ma cewa ya yi, ‘Daga Allah muke kuma gare shi za mu koma. Rashin uwa na da matukar tayar da hankali domin ita ke kwantar da hankalin danta duk lokacin da ya shiga damuwa. Abin farin ciki shi ne ta rasu ne tana aikin hajji mai girma a kasa mai tsarki, kuma ta yi shahada, kuma muna yi mata fatan Allah Ya jikanta da rahama amin.’
Moshood Sanusi Yusuf ya kara da cewa, ‘zan yi kokarin ganin na yi amfani da horarwarta, inda take horar da cewa mu rika aikita alheri kuma mu rika yi wa jama’a alheri domin mu ma a yi mana, domin ta haka ne za a gina kasa baki daya. Tana kuma horo da cewa a rika taimaka wa matalauta da gajiyayyu. Ni da yayata mu biyu kadai ta haifa, kuma lallai mun yi rashin uwa, muna fatan jama’a su sanya su a cikin addu’o’insu, da fatan mu ma mu cika da imani.’
An haifi marigayiya Hajiya Bilkisu Yusuf a ranar 2 ga watan Disambar 1952, watau tana da shekaru 62 ke nan. Sannan ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu, Fatima da Moshood, da mijinta Mustapha Muhammad Bintube.
Cikin wadanda suka je gidan marigayiyar don yin ta’aziyya sun hada da abokin aikinta Malam Muhammad Haruna da ke shugabantar kamfanin buga mujallar Citizen, mujallar da ita marigayiyar ce Edita, da tsofaffin ministoci irin su Adamu Maina Waziri da Adamu Bello, sai kuma tsohon kwamishina a Hukumar zabe Dokta Nuru Yakubu da Abdul Nasir da Jakada Aminu Wali da Muhammad Lawal Gombe da Sale Idris da Ibrahim Yakubu El-Zakzaky da Dokta Oby Ezekwesili da matar gwamnan Kaduna Hasiya Ahmad El-Rufai da Amina Muhammad da Saudatu sani da Dokta Mairo Mandara da Hajiya Farida Sada, da sauran darurruwan mutane.
Kafin rasuwarta ta taba zama Editan jaridar Truimph mallakar gwamnatin jihar Kano, kuma it ace mace da ta taba zama jaridar New Nigerian da ke da kuma mujallar Citizen. Wannan ya sanya ta zama mace ta farko a yankin arewacin kasar nan da ta rike mukamin Edita. Sannan tana yawan halartar tarurruka da gabatar da makaloli a kan al’amura dana-daban da suka shafi hadin kan kasa.