✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakkin mata a kan maza

A kowane lokaci mata na yawan yin tambayoyi a kan shin maza ne kawai suke da hakki a kan mata?  Wato su matan ba su…

A kowane lokaci mata na yawan yin tambayoyi a kan shin maza ne kawai suke da hakki a kan mata?  Wato su matan ba su da wani hakki ne a kan maza?

Da yawa daga cikin irin wadannan matan da ke yin kokari sun nuna mafi yawan rubuce-rubucen da muke yi sun fi karkata ne a kan yadda mata za su kula da maza, hanyar da mata za su mallaki maza da sauran maudu’ai da dama amma ba a tabo irin hakkin da mata suke da shi a kan mazajensu na aure.

Ko shakka babu wadannan kiraye-kiraye sun jefa ni cikin tunani ta yadda mata suke ganin kamar maza na amfani da wannan damar ce domin a danne masu hakki.

Wannan ya sa wannan fili mai farin jini na iyayen giji a kodayaushe yake kokarin ya bugi jaki sannan ya bugi taiki domin yin adalci a tsakanin jinsunan biyu na maza da mata.

A Musulunci Allah Ya daidaita maza da mata a wajen ibada da mu’amala sai fa inda aka samu sabani kamar wajen rabon gado, sallar mace a cikin gida tafi ba kamar ta namiji ba da fita yin jihadi da sauran su.

KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA YA KAMATA MAZA SU KIYAYE:

1- Namiji ya kasance mai sakin fuska ga iyalinsa.  Akwai ladubba da ya kamata magidanta su tsare a yayin shiga gidajensu kamar yin sallama tare da sakin fuska wajen shiga gida.   Sau tari wasu magidantan za ka same su maimakon sallama sai ka ga sun shiga suna harbin butoci da kwanuka da yi wa yara tsawa ta yadda daga mazan har matan sun sha jinin jikinsu ta yadda mai gida zai zama tamkar wani dan karamin zaki a gidan kowa na tsoronsa.

2- Caba ado da kwalliya:   Mafi yawan maza na da irin wannan dabi’ar ta zama cikin gida da jallabiya ko kananan kaya na hutawa har yara sun sani da sun ga mahaifin su ya yi wanka, ya caba ado to fita zai yi. A baya mata ne suka ware tsofaffin kaya na shiga dakin girki wanda kawo yanzu abun ya zama tarihi ta yadda za ka ga a yanzu mata sai sun caba ado sannan suke yin girki duk da an samu saukin kayan girki ana amfani da risho da abin dahuwa mai amfani da iskar gas da gawayi, sai maza suka fanshe su wanda su kuma matan suna da bukatar ganin mazajen su a cikin shiga ta kamala sun zauna a cikin gida ana hira.

3- Maza su rika yin shawara da matansu:   Yana da matukar mahimmanci maza su kasance suna zama da matansu domin jin kokensu da neman shawarwarinsu a kan abinda ya shige masu duhu ko ya kan taso na daga abin da ya shafi tafiyar da al’amurran gidajen su da sauran lamurran yau da kullum. Ba kamar yadda wasu ke fada ba, ana daukar shawarar mata har a aiwatar da ita a aikace domin Annabi SAW ya dauki shawarar mata kuma ya yi aiki da ita a kan sahabbansa.

4- Maza su dauki matansu a matsayin a abokaii:   Nsamiji na zama shugaba kamar yadda Allah Ya fada haka kuma yana zama aboki shi ma kamar yadda Allah Ta fada.   Sai dai abin lura kada maza su karkata waje daya su mu’amalanci mata a matsayin shugabanni kawai ba tare da wani lokacin suna daukar su a matsayin abokai na rayuwa wanda hakan zai ba mata dama su ga suna da abin fada a cikin gidajen su na aure maimakon a dauke su a matsayin bayi kawai.

5- Mata na da bukatar a yaba masu yayin da suka yi abin a yaba:   A duk lokacin da mace ta yi wani kwazo musamman na girki ko wani daga cikin ayyukan gida ko kuma ta yi ado ko kunshi ko kitso da sauran su.

Wannan abin yana sa su ji cewa lallai suna da wata irin  daraja a gidajen su kuma hakan na kara dankon soyayya a tsakaninsu da maigida.

Kadan kenan daga dimbin abubuwan da yakamata maza su kula game da matansu domin maganar gaskiya maza na da rawar da suke takawa wajen kawo matsaloli a cikin gidajensu na aure, kamar yadda suke da rawar da za su taka don kawo karshen irin wannan matsala idan ta taso.

Da fatan za mu kula tare da kare hakkin juna don samun zamantakewa mai dorewa.

Sanusi Hashim Abban Sultana

daga Jihar Katsina

08065507271

[email protected]