✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakkin tsaro ya rataya ne a kan jama’a da jami’an tsaro

Salam  Edita. A yau  ina son  in yi tsokaci ne a kan sake yunkurowar da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin Arewa maso Gabas.…

Salam  Edita. A yau  ina son  in yi tsokaci ne a kan sake yunkurowar da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin Arewa maso Gabas. A gaskiya yadda kungiyar ta sake zafafa hare-harenta a wannan yanki, yana da kyau al’ummar yankin masu fama da tabarbarewar tsaro su rika zama a cikin shirin bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar tsegunta wa jami’an tsaron duk wani wanda ba a yarda da shi ba domin ta haka ne kawai za a kawo karshen wadannan hare-hare na kungiyar a Arewa maso Gabas kasashen Nijar da Kamaru. Da fatan Allah Ya ba mu dauwammen zaman lafiya a kasashenmu na Nijar da Najeriya da Kamaru da Afirka baki daya, amin summa Amin.

 

Daga Ashiru Usman Sabuwar Gwaram, Jihar Jigawa 07030817573.