Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Hako fetur a Bauchi: Yadda mazauna yankin ke cikin kuncin rayuwa

Shugaba Buhari yana qaddamar da haqo man fetur a Bauchi
Shugaba Buhari yana qaddamar da haqo man fetur a Bauchi
  • Babu siyasa a haqo mai a Bauchi – Baru

A ranar Asabar da ta gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin fadada hako man fetur a rijiyar mai da ke kogin Kolmani da ke jihohin Bauchi da Gombe. Kogin wanda ya hade da Kogin Gongola wani bangare ne na saman Kogin Binuwai, wanda hakan ke nuna in an yi nasara za a fara hako man fetur a Arewa a karon farko.

Sai dai kuma al’ummomin kauyukan da ake aikin bincken albarkatun man fetur a jihohin biyu sun koka cewa suna fama da kuncin rayuwa, inda suka nuna fargaba kan yadda aikin ke kokarin raba su da gonakinsu.

ADVERTISEMENT

Sun ce su manoma ne da suke hadawa da kiwo, kuma babu wani abu da aka yi musu tanadi don inganta rayuwarsu. Sun ce ba su da makaranta ko asibiti, sannan an raba su da gonakinsu na noma. Sun ce sun rasa filayen noma tun lokacin da aka karbi filayensu domin fara aiki binciko man fetur sama da shekara 20 da suka gabata kuma an karba nab a tare da an biya su diyyar ko kwabo ba balle su samu damar sayen wasu gonakin da za su yi amfani da shi.

Sun ce suna farin ciki cewa akwai dimbin arzikin da aka sa ran Allah zai tabbatar a yankin idan aka samu wadataccen man fetur.

ADVERTISEMENT

Wata mai suna Ladi Naboth ta ce “Mu mazauna kauye ne, kowa ya san noma shi ne sana’armu ba za mu ci abinci ba in ba mu yi noma ba, ga shi an amshe mana kasar noma. Mun roke su su taimake mu su ba mu gonakinmu ko su biya mu diyya. Duk da cewa mun yi murnar samun wannan arziki, amma a sani ba za mu amfana da shi ba sai muna raye. Su ba mu diyyarmu mu ci abinci mu rayu don mu mori arzikin man.”

Shugaban Kamfanin NNPC Injinya Maikanti Baru yana yi wa Shugaba Buhari bayani kan aikin haqo mai a Bauchi a gefensa gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe ne suke sauraro
Shugaban Kamfanin NNPC Injinya Maikanti Baru yana yi wa Shugaba Buhari bayani kan aikin haqo mai a Bauchi a gefensa gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe ne suke sauraro

Ta ce bayan an biya su diyya suna bukatar a gina musu asibiti domin a yanzu sai sun tafi Asibitin Pindiga ko Gombe a Jihar Gombe ko Alkaleri a Jihar Bauchi kafin su sami magani. Ta ce haka mata masu nakuda suke fama. “Da nakuda ta kama ni dole aka dauke ni a kan babur aka kai ni asibitin garin Pindiga wanda ke da nisan sosai kafin aka karbi haihuwata, kuma muna da makaranta amma babu malamai a ciki a kawo mana malamai domin su karantar da ’ya’yanmu don muna son ’ya’yanmu su yi ilimi,” inji Ladi.

Malam Haruna Adamu wani manomi kuma makiyayi a kauyen Barambu da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi ya ce, filin da ake aikin hakar man filayensu ne da suke noma a ciki. An samu albarkatun kasa a wajen, amma masu aikin ko gwamnati ba ta biya su diyya ba har zuwa yau.

“Sannan ana aikin nan mu jama’ar wannan kauye an mai da mu ba mu da wani amfani, domin ba mu cin gajiyar aikin da ake yi, sai dai wdanasu su zo su ci arziki, ba su nemanmu ko da aikin leburanci ne, sun kuma hana mu yin noma a filin,” inji shi.

Malam Haruna ya ce, sun yi tuntuba sau da dama, sun bi sawu amma an ki a biya su diyya.

Ya ce ya fi shekara talatin yana noma a filin, “Ba za mu zauna babu abincin ba, yanzu na samu dan wani karamin fili ina noma a kauyen Fandako amma abin da nake nomawa ba ya isataa. Haka akwai daruruwan mutane irina da wannan abu ya shafa,” inji shi.

Ya ce duk da suna murna da wannan ci gaba da kasa ta samu, amma ya dace a dube su da idon rahama, “Muna murna sosai da wannan ci gaba, amma muna kuka sosai, saboda haka muna kira ga gwamnati ta shigo cikin lamarin, domin tausaya mana,” inji shi.

Altine Alesha wacce ta koka kan mawuyacin halin da suke ciki a yankin, ta ce “Gonakin da mazanmu suke nomawa an amshe an kama aikin mai ba tare da lura halin da za mu shiga ba. Ko a bana an hana mu yin noma gaba daya a wajen, kuma bara sun zo sun share filayen suka ce za su biya diyya idan an fara aikin, ga shi an jima da fara aikin amma har yanzu ko sisi ba mu gani ba. An kai takardunmu, an shigar da su an ce za a biya amma har yanzu ba a biya mazanmu ba, rayuwarmu tana kara shiga cikin kunci da wahala.”

Altine ta ce su mazauna kauyen ba su cin gajiyar wani abu na dimokuradiyya, “Kuma dan noman da muke yi ma an zo an kwace filaynenmu an kuma hana mu filayen ko diyya. Muna kira ga gwamnati ta shiga cikin lamarin a taimaka mana ba mu yi noma ba, ba mu da abincin da za mu ci, muna cikin kunci,” inji ta.

Da yake tsokaci kan  zargin masu filayen, daga cikin masu Yan kwangila da ake aiki awajen da ya nemi ‘yan jarida su sakaye sunansa ya shaida cewar su kara hakuri za a biyasu hakkinsu, “batun biyan kudin diyya na wannan filin na hanun (APS) da ke karkashin NNPC. Don haka kudin na hanun kamfanin NNPC. Amma gaskiya ko mu muna jin zafin rashin biyansu kudinsu amma su kara hakuri za a biyasu.

“Hakkin biyan kudin diyyar wadanda aka amshi filin nan a hanunsu yana hanun gwamnati ne, ba a hanun Yan kwangilaba, don haka su bi a hankali za a biyasu kamar yadda gwamnatin take maganar za a zo a tantance wadanda aka shiga filayensu da gonankinsu.