✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakora da karfe sun makale masa a makogwaro na kwana takwas

Wani tsoho da aka sakaya sunansa mai shekara 71 ya yi kwana takwas da wasu hakaro da karfe a cikin makogwaronsa, sai da likitoci suka…

Wani tsoho da aka sakaya sunansa mai shekara 71 ya yi kwana takwas da wasu hakaro da karfe a cikin makogwaronsa, sai da likitoci suka yi masa tiyata kafin a gano abin da ya makale masa.

Rahoto ya ce ba wannan ne karo na farko da hakora suka taba makale masa ba. Wannan mutum tsohon ma’aikaci ne da yake karbar fansho a yanzu, an dai samu nasarar cire masa hakoran gaba guda uku da suka makale masa tare da wani faifan karfe

Mutumin ya kai kwana shida bai iya hadiye abinci duk abin da ya sa a baki sai ya fara zubar da jini a cikin bakinsa wanda hakan ya zamar masa abu mai wahala wajen hadiye abincin.

A cewar rahoton mujallar kiwon lafiya ta BMJ, da farko an rubuta wa mutumin maganin rage radadin ciwo da ciwon ya ci gaba sai aka yi masa gwaji ta hanya zura abin da zai dauki hoton makogwaronsa zuwa inda yake numfashi don sanin abin da ke damunsa daga bisani sai likitocin suka yanke shawarar yi masa tiyata.

Bayan kwana biyu sai dattijon ya sake komawa inda aka ce ya sayi magani ya sha, sakamakon tsananin zafin ciwon, har ta kai ga bai iya hadiyar kwayar maganin da aka rubuta masa da kuma zargin yana dauke da cutar nimoniya.

Likitocin sun gano cewa, akwai wani faifan karfe da yake dakatar duk wani abu da zai hadiya a makogwaronsa. Rahoton ya ce, mutumin ya sanar da likitocin cewa akwai wasu hakoransa da suka fada cikin makogwaronsa kafin a yi masa tiyata da kwana takwas

Hoton cikin jikin dan Adam na ‘D-rays’ ne ya tabbatar da cewa, akwai abubuwan da suka hana marar lafiyar hadiyar abinci, sai da aka yi masa tiyata aka cire su bayan kwana shida kuma aka sallame shi daga aibitin.