Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Halilu Ahmad Getso: Yadda malamin gona ya zama dan jarida

Alhaji Haliliu Ahmed Getso
Alhaji Haliliu Ahmed Getso

Alhaji Haliliu Ahmed Getso ya fara aikin jarida a matsayin mai daukar rahoto, inda ya rika bin matakai daban-daban har ya kai matsayin Shugaban Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilin da ya sa aka cire shi aka canza masa wurin aiki zuwa Legas. Dan jaridar kuma ya bayyana cewa duk da cewar a yanzu ya kai shekara 70, a shirye yake ya gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo da sauran batutuwa.

Yaya rayuwa ta kasance daga haihuwa zuwa yau?

ADVERTISEMENT

Zan iya cewa alhamdu lilahi da irin rayuwar da na samu kaina a ciki. Duk da kasancewata ba kowa ba, sai ga shi harkar aiki ta sa na zama wani, inda zan yi magana kowa ya saurare ni. Na fara da neman ilimin Alkur’ani, sannan na shiga karamar makarantar firamare da ke garinmu Getso a 1958, inda na yi aji uku. Daga nan sai na tafi babbar firamare, na karasa ragowar aji hudu a can. Bayan na kammala sai na tafi makarantar Sakandaren Birnin Kudu. A lokacin makaranta biyu ce kawai a duk fadin Kano, wato Kwalejin Rumfa da Kwalejin Gwamnati ta Dawakin Kudu. Mun yi karatu na tsawon shekara hudu da watanni sabanin shekara biyar da yake a cikin tsarin sakamakon babu kayan aiki tun daga kan ajujuwa da dakunan kwanan dalibai da malaman kansu. Sai dai hakan bai sa mun zama koma-baya a karatu ba, domin zan iya cewa tunda ake yaye dalibai a wannan makaranta ba a taba samun daliban da suka shahara kamar ’yan ajinmu ba. A cikinmu akwai Dokta Junaidu Muhammad, wanda ya taba zama dan majalisa a lokacin mulkin Shagari da akwai Dokta Bashir Dankadai, Hakimin Tudun Wada da Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Na so in je jami’a sai dai hakan bai yiwu ba saboda dalilai biyu. Na daya mahaifina ya rasu tun ina shekara 11 da haihuwa, duk da cewa alhamdu lillahi kawunmu ya ci gaba da kula da mu. Na biyu kuma ina so in fara aiki don in rika samun dan albashin da zan taimaki kaina da ’yan uwana. To dama lokacin muna makaranta Gwamna Audu Bako ya kawo wani shiri na bunkasa ayyukan noma don haka aka nemo daliban makarantun sakandare don horar da su a kan ayyukan gona. Bayan ya gama yi mana lacca a kan haka sai muka bayar da sunayenmu. Wadansu daga cikinmu an kai su Makarantar Ayyukan Gona ta Samaru da ke Zariya, yayin da wadansu aka kai su wata makarantar da ke Kabba (a Jihar Kogi). An koyar da mu, inda ake ba mu abinci sau uku da dakin kwana har ma ana ba mu albashi kamar dai alawus. Ina daga cikin wadanda aka kai Zariya, duk da cewar ban kammala ba sakamakon rashin fahimtar da muka samu da wani malami, inda ya shigo aji ni kuma ina karatun haridar New Nigerian. Ya gaya min maganganun da ba zan iya jurewa ba, don haka na mayar masa da martani, kuma na fice daga ajin. Wannan ya faru saura wata uku mu kammala karatun.

ADVERTISEMENT

Wani akasi da aka samu, sai na ga talla a jaridar cewa ana neman ma’aikata, wadanda za su rika aika wa jaridar da labarai daga Arewa. Dama ina da burin in zama ma’aikacin gidan rediyo, don kawai na rika yin shirin ‘Zabi Sonka.’ Lokacin da na ga waccan talla sai na yago takarda na rubuta takardar neman aiki, na hau kekena na je na kai gidan waya da ke Samaru. Na kuma yi sa’a cikin mako guda na samu amsa, a cikin kasa da mako biyu na samu takardar daukar aiki, inda na fara aikin jarida a 1979.

Wane aiki ka fara lokacin da aka dauke ka aiki?

Ai takardar aikin ta bayyana abin da aka dauke ni a kai. Ranar farko da na fara aiki an hada ni da mai gabatar da shiri mai suna Idris Garba. Yana da kirki, domin ya nuna min duk abin da ya kamata in sani. Na zauna kwana uku aka mayar da ni wani wurin kuma. Tsarin aikin a lokacin duk sabon ma’aikaci sai ya zauna a kowane sashe na gidan, domin ya samu ilimi a kan aikin. Sashe na karshe da ma’aikaci zai je shi ne na kasuwanci, daga nan mutum zai san matsayinsa ko ya iya, idan kuma bai iya ba su yi waje da shi.

An tura ni bangaren shirye-shirye, daga baya kuma sai sashen labarai da al’amuran yau da kullum. An horar da mu a dakin taro na Lugard da ke Kaduna, inda kwararrun ’yan jarida suka koya mana yadda ake gudanar da aikin, inda daga nan aka kai mu jihohin da za mu yi aiki. Ni ne farkon wanda ya fara aika wa Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna labarai daga Kano. An bar ni ba masauki, ba ofis babu kuma wani jagora da zai nuna mini aikin. Abin da aka yi shi ne, an hada mu da Ma’aikatar Watsa Labarai, inda idan za su fita aiki mukan bi su don kalato abin da ya faru tare da rubuta shi a matsayin labari, sannan mu aika da shi Kaduna. A wancan lokaci hanyar sadarwa tana da wuyar samu. Samun tarho da za ka yi amfani da shi ba abu ne mai sauki ba. Ina yin amfani da tarho dinsu sai dai wani lokacin yadda lambar za ta shiga ma abu ne mai matukar wuya.

Wane kalubale ka fuskanta kasancewar ka samu horo a kan aikin gona sai kuma ga shi ka samu kanka a harkar jarida?

A lokacin na samu kwararrun abokan aiki a Kano, wadanda suke a jaridu daban-daban, duk da cewa akwai kishi a tsakanin jarida da kuma rediyo, kasancewar rediyo daga baya ya zo amma kuma an fi saninsa. Haka na zauna a Kano na yi shekara biyu, daga baya na koma Kaduna. A can na iske sabon ma’aikaci Alhaji Musa Karaye, wanda yana da digiri sai dai kuma shi ba dan jarida ba ne. Haka kuma malamina ne a makarantar firamare. Ya zauna a can tsawon wata uku daga baya aka mayar da shi Kano a matsayin babban mai rahoto. To, ganin cewa na zauna a Kano na san wani abu a kan aiki, don haka ya roki a kai ni Kano a matsayin mataimakinsa. Haka ne ya sa muka dawo Kano.

A wannan lokaci ne muna hayar ofis a kan titin Ibrahim Taiwo, sai dai shi Alhaji Karaye bai dade ba daga baya ya shiga harkar gwamnati. Daga baya sai na fara sha’awar yin aiki da gidan Rediyon BBC. Don haka muka tattauna da su, suka amince zan yi musu aiki a kan wasu sharudda. Kafin na kai ga sanya hannu a kan yarjejeniyr sai ga wata damar ta samu, inda gidan rediyonmu ya samu gurbi guda biyu, aka ba ni daya na tafi kasar Holland, na yi wani kwas a wata makarantarsu ta koyon aikin jarida, wadanda suka dauki nauyinmu. An ba ni zabi tsakanin wuraren biyu, sai dai bayan na tattauna da mutane sai na tafi kasar Holland saboda shi dama ce da ke zuwa lokaci-lokaci, amma BBC yana nan koyaushe.

A karshen kwas din kasar Holland tana ba mutum dama ya zabi kasa daya a Turai ya kai ziyara. Don haka na zabi Ingila, inda suka dauki nauyin tafiyata gaba daya. Wannan ziyara ta ba ni dama na je BBC, muka sake kulla yarjejeniyar aiki. Bayan kamar shekara biyu da dawowata Najeriya sai BBC suka zo suka nemi in je in yi aikin shekara uku, sai dai Gidan rediyon Tarayya na Kaduna bai amince na yi shekara uku ba sai dai sun ba ni shekara daya da rabi don samun horo. A nan BBC ya amince, sai dai bayan na je can kasar ba su horar da ni a matsayin ma’aikacin kwantaragi ba, sai suka ba ni horon cikakken ma’aikaci. Sai dai ban zauna na cika wannan wa’adin shekara daya da rabi ba saboda ba zan iya jure wulkancin Turawa ba, saboda kabilanci, mun sha fama da rashin ’yanci. Don haka na bar aikin kafin wata uku da karewar wa’adin kwantaragin nawa. A lokacin na yi abin da ba a taba yi ba, domin na tafi garin da matana biyu. A tsarinsu mace daya za ka tafi da ita don haka sai da suka je suka nemo min izini in shiga da mata biyu tare da ba ni dukan abubuwan da nake bukata.

An cire ka daga mukaminka na Shugaban Rediyon Tarayya na Kaduna, inda aka mayar da kai Legas. Me ya jawo haka?

Rashin fahimta ce ’yar kadan da muka samu tsakanin ni da Alhaji Mamman Shata a 1995. Mun shirya wasan Kalankuwa don mu samu kudin shiga. Muka kafa kwamiti, inda ya zo mana da tunanin shirya Kalankuwa a garuruwan Kano da Zariya da Funtuwa. Mun samu nasarar gudanar da na Funtuwa sai da muka zo yin na biyu a Zariya, inda muka gayyaci mawaka ciki har da Mamman Shata da Musa Danbade. Sai dai mun samu labarin cewa mutanen biyu ba su shiri don haka sai muka yanke cewa daya daga cikinsu ya zo ya yi wasa da safe wani kuma ya zo ya yi da yamma. Muka aika musu takardar gayyata suka amince za su zo. Na aiki ma’aikacinmu wanda kuma suna shiri da Shatan, wato Mustapha Umar Misau ya kai wa Shata takardar gayyata, wanda kuma ya amince zai halarta. Lokacin da ya rage saura mako biyu sai na sake aika wani daga cikin manajojina wato Bashir Mustapha wurin Shata don ya tuna masa, inda ya sake nanata zai zo. Saura kwana tara a yi wasan ni da kaina na je har gidansa a Funtuwa don tunatar da shi, inda kuma ya yi min alkawarin zuwa. Sai dai abin takaici Shatan da Danbade babu wanda ya zo a cikinsu. Saboda kin zuwan da suka yi sai ga shi wadansu fusatattun matasa suka yi yunkurin kona wurin. Amma Allah Ya taimake mu muka shawo kan lamarin. To lokacin da muka yi taro kan abin da ya faru sai muka yanke shawarar a daina sanya wakokinsu a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna har sai sun zo sun gaya mana kwararan hujjojinsu na rashin halartar wasan tare da neman afuwa  a kan abin da suka yi. Bayan kwana biyu sai Danbade ya zo ya bayar da hakuri, inda ya ce daya daga cikin makadansa ne ya rasa babban dansa, wanda kuma ya ga ba daidai ba ne ya zo ya yi wasa a daidai lokacin da iyalin mamacin ke zaman makoki. To mun yi masa uzuri, amma shi Shata ba wai kin zuwa ba mu hakuri kawai ya yi ba sai, ga shi kuma yana zuwa wurare daban-daban yana cika baki cewa wai ba mu samu kudi ba saboda rashin halartarsa Kalankuwar da muka shirya. Bayan an yi watanni ba a sanya wakokinsa a gidan rediyo sai mutanen gari suka fara surutu a kan haka. Shi kuma Shata sai ya fahimci cewa farin jininsa yana raguwa, sai ya fara neman hanyar da zai yi sulhu da mu. A wancan lokaci ne ya samu Alhaji Dankabo ya gaya masa damuwarsa.

Wata rana sai Alhaji Dankabo ya kira ni Abuja ya nemi na dage wannan takunkumi a kan Shata, ni kuma na nuna masa hakan ba zai yiwu ba. To daga nan ne sai wadansu suka yi masa hanya ya je ya ga matar Shugaban Kasa Hajiya Maryam Sani Abacha.

Daga nan ne ita kuma ta bar komai a hannun Mashawarcin Shugaban Qasa Kan Harkar Tsaro Alhaji Isma’ila Gwarzo don ya kula da lamarin. A wannan lokaci ne suka umarci Darakta Janar xinmu Alhaji Abdurrahman Michika da ya cire ni a muqamina tare da tura ni wani waje na daban. Wannan ne ya jawo aka kai ni Legas.

A wancan lokaci Gidan Rediyo Tarayya na Kaduna yana da qarfinsa sai dai daga baya, ya zama wani abu daban, akwai zarge-zargen cewa gwamnati tana sane ta bar wurin ya lalace mene ne ra’ayinka a kan haka?

Idan wani abu ya faru mai kyau ko akasinsa, to dole akwai wani wanda ya janyo abin. Idan abu mai kyau ne sai ka ga mutane suna so su ce su ne suka yi, amma idan ba shi da kyau sai ka ga mutane suna xora zargin a kan waxansu. Gaskiya abin da ya faru da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna ba abu ne da ya faru lokaci guda ba, A wancan lokaci babu wani ma’aikaci da zai yi maka qorafi a kan rashin samun haqqinsa. Wani abin ma ba ka san da shi ba za a kira ka. A wancan lokaci idan mutun ya yi kuskure a take za a nuna masa kuskurensa, idan ma ya kama a kore shi ne za a yi hakan ba tare da wani ya nemar masa sauqi ba.

A wani lokaci akwai wani Gwamna ya je ya samu Modibbo tare da neman ya cire xan jaridar da ke ofishinsa na gidan gwamnati amma hakan bai samu ba, saboda ya gaya masa cewa ba wai Gwamna yake yi wa aikin shi kaxai ba, yana yin aiki ne ga sauran mutanen jihar kuma babu wani da ya zo ya yi mana qorafi a kan rahotanninsa, don haka ba a cire shi ba.

Wani abin takaicin shi ne yadda ’yan jaridar yanzu musamman na rediyo ke gudanar da aiki, domin ya bambanta da na baya. Za ka samu xan jarida yana karanta labarai yana cakuxa qare-qaren harsunan garuruwa daban-daban.

Gwamnati ta taka rawa wajen musamman ta fuskar tsarin shugabancin gidan. Wannan shi ya jayo gwamnati ta lalata gidan rediyon. A wancan lokaci ko gwamnati ba ta da ikon juya harkar gidan gaba xaya.

Ka riqe muqamin Shugaban Rediyon Tarayya na Kaduna har sau biyu, wane qoqari ka yi don gyara waxancan kura-kuran?

Lokacin da aka naxa ni wannan muqami na tarar wurin a hargitse, domin ana bin gidan bashin sama da Naira miliyan 50. Ga bashin NEPA da na NITEL sun taru fiye da zaton mutum. Ga bashin da masu kawo wa gidan man dizal. Sai dai kafin a cire ni sai da na yi qoqari na biya dukan bashin da ake bin gidan tare da tara wasu kuxin da suka kai tsakanin Naira miliyan bakwai zuwa miliyan goma.  Mutumin da ya gaje ni yana nan da ransa idan qarya nake yi ya fito ya qalubalance ni.

Har yanzu kana gudanar da aikin jarida?

Kowane lokaci wani ya nemi in gabatar masa da wani shiri zan yi. Nan ba da daxewa ba zan yi wani shiri mai suna Iyabo. Wannan shirin zai nuna rayuwar Tsohon Shugaban Qasa Olusegun Obasanjo, mutane za su samu damar sanin ko shi wane ne. Zan samu mai xaukar nauyinsa kafin lokacin.

Wace shawara za ka bayar ga ’yan jarida masu tasowa?

Ina shawartarsu da su ji tsoron Allah wajen gudanar da aikinsu. Su zama masu riqo da gaskiya da riqon amana a duk abin da suka sanya gaba. Idan suka yi haka na tabbata za su yi fice a cikin aikin.