✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halilu Akor: Masanin kasuwanci da ke yi wa mata kitso

Halilu Akor wani matashi ne da ya karanta harkokin kasuwanci amma yake yi wa mata kitso da gyaran gashi a cikin garin Lafiya fadar Jihar…

Halilu Akor wani matashi ne da ya karanta harkokin kasuwanci amma yake yi wa mata kitso da gyaran gashi a cikin garin Lafiya fadar Jihar Nasarawa. A zantawarsa da wakilinmu ya fadi alfanu da yake samu, kuma ya shawarci matasa su daina tsaywa neman aikin gwamnati su  shiga kasuwanci ko su kama sana’a don tsare mutuncinsu:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Halilu Akor. Ni dan Jihar Kogi ne. Na kammala karatuna a Kwalejin Kimiya da Kere-Keer ta Jihar Benuwai inda na karanta harkokin kasuwanci. Da na kammala ne sai aka turoni nan Jihar Nasarawa don hidimar kasa a shekarar 2015. Bayan na kammala sai na yanke shawarar ci gaba da zama a nan garin Lafiya don bude shagon gyara gashi da yin kitso ga mata.

 

A ina ka koyi kitso da gyara gashin?

A gaskiya da farko a rayuwata ban taba tunanin zama mai kitso da gyaran gashin kan mata ba. Amma kamar yadda ka sani rayuwa a kasar nan sai a hankali. Muna wani lokaci ne da idan ka ce za ka tsaya neman aikin gwamnati da wuya ka samu. Shi ya sa na shiga kitso da gyara gashin mata don dogara da kaina kafin lokacin da Allah zai ba ni aikin gwamnati. Don ka ga bayan na kammala hidimar kasa, na yi ta jiran aikin Gwamnatin Tarayya da wani baffana ya yi min alkawari. Amma daga baya na fahimci ba alamun samun aikin bayan kimanin wata 6 da ya yi min alkawarin na kuma nemi aiki a wurare ban samu ba. Sai na ce don me ba zan fara wani kasuwanci ko wata sana’a ba komai kankantarta ba maimakon ci gaba da bata lokaci ina jira aikin gwamnati. Kuma kasancewar na kware a gyara gashin kai tun ina zama da wani baffana lokacin ina makarantar firamare, ina yi wa mutane gyaran kai ana biyana, sai na ce bari in gwada. Kuma a gaskiya ina samun na biyan bukatuna na yau da kullum. Shi ne kawai na fara yi wa mata.

 

Yaya kake ji kai namiji amma kana yi wa mata kitso da gyaran gashi?

Ka ga wani abin mamaki shi ne yadda yawancin mata suka fi so namiji ya gyara musu gashin kansu maimakon ’yan uwansu mata. Wadansu daga cikinsu da ke shakka da zarar na kammala musu gyara za ka ga suna mamakin aikina kuma su ci gaba da zuwa. Kuma a kowane lokaci ina kasancewa cikin farin ciki da annashuwa kasancewar wadannan abokan cinikina suna da hankali kuma ba su da matsala. Kuma mukan yi wasa da dariya da su wanda hakan ya sa na koyi abubuwa da dama.

 

Akalla nawa kake samu a rana?

A gaskiya duk da cewa ban so in bayyana kudin da nake samu a yini daya ba, saboda wadanda labarina zai sa su koyi sana’ar zan iya bayyana maka cewa ina samun daga Naira dubu 60 zuwa dubu 70 a kowane wata. A lokutan bukukuwa kuma nakan samu fiye da haka.

 

Akwai kalubalen da kake fuskanta?

Babban kalubalen da nake fuskanta a yanzu shi ne na kudi. Domin ina so in bunkasa harkata fiye da yadda take a yanzu. Amma ba ni da jarin yin haka. Na biyu kuma shi ne kalubale da nake fuskanta a wajen wadansu abokan huldata mata. Don kamar yadda na bayyana maka a baya yawancinsu ba su da matsala amma akwai wadansu da sha’aninsu sai a hankali. Za ka ga suna nuna maka kyama suna ganin bai dace namiji ya taba musu kai ba. Wadansu kuma ka ga suna yi maka kallon raini suna dauka cewa mutuwar zuciya ce ke sa namiji yin kitso da gyaran gashin. Hakan a gaskiya na ba ni mamaki da takaici a wasu lokuta. Sai dai idan muka fara hira da ire-irensu da ke da irin tunani, na sanar da su cewa na kammala karatu sai ka ga suna ba ni girma su kuma jinjina mini. Kuma a nan ina so in bayyana maka cewa irin wannan hali ne ke illata al’umma. Don gwamnati kadai ba za ta iya bai wa kowa aiki ba idan mutum ya kama sana’a ko kasuwanci kuma aka rika masa kallon raini da wulakanci da sauransu. Dole al’umma su sauya irin wannan tunani idan muna son samun ci gaba a kasar nan.

 

Idan ka samu jarin da kake nema yaya za ka bunkasa sana’arka?

Ka ga abu na farko da zan yi shi ne zan dibi matasa ’yan uwana da dama da ke neman aiki don in koya musu. Kuma wadanda zan fi diba su ne wadanda ke hidimar kasa. Duk wanda ke da sha’awar sana’ar na sha alwashin koyar da shi don su ma wata rana su koya wa wadansu ba tare da kowa ya dogara da gwamnati ba. Ka ji kadan daga cikin yadda zan bunkasa sana’ata ke nan da zarar na samu dama.

 

A karshe wace shawara kake da ita ga matasa musamman wadanda suka kammala karatu suna jira aikin gwamnati?

Shawarar ita ce su daina dogara kacokan ga aikin gwamnati. Lokacin yin haka ya riga ya wuce. Kowa ya yi sana’a ko kasuwancin da zai iya. Su kuma rika dogara ga Allah don wurinSa ne kawai za su iya samun tabbaci a rayuwarsu.