✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da kasa ke ciki: An rufe mana baki – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce sarakuna da malaman addini da ya kamata…

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce sarakuna da malaman addini da ya kamata su rika sanya ido kan shugabannin siyasa wajen suna yin abin da ya dace, an rufe musu baki.

Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Tattaunawa a Tsakanin Addinai kan Zaman Lafiya karo na Uku na bana da aka gudanar a Abuja.

Taron ma taken “Tattaunawa a Tsakanin Addinai: Karfafa Al’adar Zaman Lafiya da Adalci da Sulhuntawa, Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya wakilce shi a taron.

Ya ce: “Duk wanda ya kashe wani Kirista ko Musulmi mai aikata babban laifi ne kuma a haka ya kamata a dauke shi. Duk abin da nake ji a yau mamaya ce. Sarakuna da shugabannin addini da ya kamata su  sanya ido kan shugabannin siyasa don su aikata daidai ga jama’a,  an tilasta su yin shiru. Idan kai sarki ne ka faye yin magana sai a cire ka. Idan kai liman ne ko Bishop kana bukatar kudin sadaka; sai ka shirya yin harka da Shaidan ta yadda za ka samu kudin sadaka.”

Sarkin Musulmin ya ce babu wani fada a tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya, inda ya ce jahilci a kullum yake jawo takaddama da tayar da jijiyar wuya da sunan addini a kasar nan.