✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin Kirki

Godiya ta tabbabta ga Ubangiji Allah mai iko duka. Barkan mu kuma da sake saduwa cikin wannan makon. A wannan makon za mu yi nazari…

Godiya ta tabbabta ga Ubangiji Allah mai iko duka. Barkan mu kuma da sake saduwa cikin wannan makon. A wannan makon za mu yi nazari ne akan zama da halin kirki.

Rashin hakurin, fushi, zamba, son kai, da makamantan su, sun hana mutane da dama nuna halin kirki ga juna a yau , nuna halin Kirki abu ne mai sauki idan mutum na da kaunar Ubangiji Allah cikin zuciyarsa, kamar yadda zamu gani cikin littafin Luka 10:27; Sai ya amsa ya ce, “Ka kaunaci Ubangiji Allahanka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan karfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma kaunaci dan’uwanka kamar kanka.” Lallai ne idan mutum na da kaunar Allah a zukatarsa zai so dan’uwansa zai kuma nuna halin kirki ga jama’a, domin “kauna tana sa hakuri da kirki. kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura.  kauna ba ta sa daga kai ko rashin kārā, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko.  kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. kauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da ban gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali”(1 Korantiyawa 13:4-7). Ba zaka sami halin kirki a wurin da ba kauna ba, shi ya sa littafi mai tsarki na koya mana hanyar nuna kauna ga junanmu ta wurin kaunar Ubangiji da dukan ran mu da kuma karfin mu.

Babu shakka a cikin harkokin mu na yau da kullum mutane kan iya saba mana ta hanyoyi da dama, yakan zama da wuya mu nuna halin kirki cikin irin wannan yanayi, amma idan muka dubi rayuwar manzo Bulus cikin wasikarsa ga ikkilisiyar Allah a Koranti; 2 Korantiya 6:4-6; “Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matukar jurewa, da shan wahala, da kuntata, da masifu, da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.  Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da hakuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar kauna,” Ubangiji Allah zai bamu nasara. kada mu ji tsoro ko mu dauki irin wannan tsanani ya zama mana dalilin rashin nuna kirki ga jama’a, ba haka Ubangiji Yesu Almasihu ya nuna mana ba da yana nan duniya, mu yi koyi da rayuwarsa, mu bi gurbin da ya nuna mana.

Idan har kana kiran kanka Kirista wato mai bin Yesu Kristi na gaske, lallai ne fa ka zama mai bin gurbin da ya bar mana, shi ya sa Ruhu mai tsarki ya bayana mana a fili halin mutuntaka da Albarkar Ruhu cikin littafi mai tsarki don ya jagorance mu. Yesu Almasihu ya yi zaman tsarki da kauna – har ma ga makiyansa, bai kaunaci ko kuwa nuna kirki ga almajiransa kadai ba, ya so dukan jama’a, (Sa’ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?” Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya”. Matiyu 9:10-12). A wuri aiki, a hanya, kasuwa ko a gida kana nuna bambanci wurin yin kirki ga wani don shi ba danuwanka ba? A rayuwan mu na yanzu zaka ga mutane na nuna bambancin kabila, addini, jim’i, da dai makamantan su, wannan ba daidai ba musamman idan kana kiran kanka Kirista, ta wurin nuna Kirki ga mutane musamman wa’yanda basa kaunar ka, rayuwan ka zai zama abin koyi a garesu har ma zasu sami tsira daga irin wannan halin mugunta, domin littafi mai tsarki bai koya mana rama mugunta da mugunta ba (1 Bitrus 3:9; Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka). Idan kana cike da halin kauna da Kirki Ubangiji Allah zai goya maka baya cikin duk abin da ka ke yi, ba zai kuma bar magabci ya ci nasara bisa kanka ba – don kana bin tafarkinSa.

Mafi muhimmanci shi ne rayuwa cikin Ruhu, ta wurin yin haka ne zamu sami nasara cikin rayuwan da zai gamshi Ubangiji.  Romawa 8:9; Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.