✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hallaka ’yan sanda: Ana neman lauyan Nnamdi Kanu ruwa-a-jallo

Rundunar ’Yan sandan Najeriya da ke Jihar Anambra ta ayyana neman lauyan Shugaban Kungiyar Neman Kafa Kasar Biyafara (IPOB), Barista Efeanyi Ejiofor, bayan da aka…

Rundunar ’Yan sandan Najeriya da ke Jihar Anambra ta ayyana neman lauyan Shugaban Kungiyar Neman Kafa Kasar Biyafara (IPOB), Barista Efeanyi Ejiofor, bayan da aka zargi ’ya’yan kungiyar  da kashewadansu manyan jami’an ’yan sanda biyu tare da kone gawarsu a motarsu

A ranar Litinin ce aka kashe jami’an biyu kamar yadda wata sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra SP Haruna Muhammad, ta bayyana. Ya ce, jami’an sun isa yankin ne bayan koken da aka shigar kan Barista Efeanyi Ejiorfor, wanda ya tsaya wa shugaban Kungiyar IPOB, Nmandi Kanu. Ya ce wadanda ake zargin ’yan Kungiyar IPOB ne sun far wa ’yan sandan da harbi da bindiga da sara da adduna lokacin da suka je kama lauyan bayan ya ki amsa gayyatar da rundunar ta yi masa,  inda  suka hallaka ’yan sanda biyu suka  kone gawarsu yayin suka jikkata wadansu da dama.

Rundunar ’yan sanda ta bayyana sunayen manyan jami’anta da suka rasa rayukansu da suka hada da Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Oliber Abbey, wanda shi ne Kwamandan Yanki na Oraifite, sai ASP Joseph Akubo Kwamandan Rundunar Yaki da Fashi da Makami ta SARS.

A nata bangaren haramtacciyar kungiyar ta IPOB, ta musanta hannu a kisan ’yan sandan inda ta zargi ’yan sanda da hallaka ’yan kungiyar biyu tare da lalata gidan lauyan jagoransu.

A wata sanarwa da Kungiyar Ibo ta Ohaneze ta fitar a ranar Talatar da ta gabata da shugabanta John Nwodo ya sanya wa hannu, ta yi tir da farmakin da ta ce, ’yan sanda sun kai a gidan Lauya Ejiorfor, inda ta bukaci doka t ayi aikinta a kan lamarin.