✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hambararren Shugaban Afirka ta tsakiya ya fice daga Kamaru cikin sirri

Hambararen Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize, wanda ya dinga zaman gudun hijira a Kamaru ya fice daga kasar, kuma ba a san hakikanin…

Hambararen Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize, wanda ya dinga zaman gudun hijira a Kamaru ya fice daga kasar, kuma ba a san hakikanin inda ya nufa ba. Shugaban ya ficene  daga Kamaru kwanakin kadan bayan sababbin hukumomin Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika sun fara farautarsa, tare da tuhu7marsa, bisa ga zargin aikata laifuffuka da suka ce ya yi a lokacin mulkinsa.
 A ranar 24 ga watan Maris ne Hadakar kungiyoyin SELEKA karkashin jagorancin Michel Djotodia suka kwace mulki daga hannun Bozize. Don haka ya ketare zuwa Kamaru tun wannan lokacin. Hambararen Shugaban ya tashi ne a cikin sirri daga filin jirgin sama na Yaounde zuwa wani masaukin da har yanzu ake ta tantama akai. Shugaban tare da iyalinsa sun fice daga Kamaru ne a cikin jirgin sama na Kenya Airways da aka kira Makuranta a Nairobi ne a kasar Kenya.
Wata majiyar ta bayyana cewa, Bozize ya tafi kasar Afirka ta Kudu, inda wasu kuwa suka fifita cewa ya zarce zuwa kasar Benin. Ko da yake kuma wasu masu sharhi na fassara cewa wannan tafiya tashi, Gwamnatin Kamaru ce ta shirya domin ta rabu da nauyin kayan nauyin daukar dawainiyarsa da ke rataye a kanta
Masu sharhi na ganin matsin lamaba Kamaru ta sha daga bangaren wasu kasashe da suka hada da Chadi, musamman ganin cewa kasancewar Francois Bozize a cikin wata kasa da ta yi  iyaka da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ba wata alama ba ce na cewa za a samu dorewar kwanciyar hankali. An dai karkare takaddama ficewar Francois Bozize da  cewa ya tafi halartan wani taron
wata darikar da yake bi a birnin Nairobi na kasar Kenya.
A duk tsawon kusan watanni 3 da Francois Bozize ya yi a Kamaru, ya fara zama ne na wasu a Hilton Hotel gabannin ya kaurace izuwa makwabtakan Paul Biya, kusa da Fadar Shugaban kasa a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2013, shi ma Francois Bozize ya kwace mulki ne a hannun Ange Félid Patassé.