Da Dumi Dumi

…Hana alamjiranci babban bala’i ne – Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Bauchi

Me Shehi zai ce kan yunkurin da ake yi na hana almajiranci a Najeriya?

Muna jin kishin-kishin cewa wai gwamnati za ta hana almajiranci da bara. Wannan babban bala’i ne zai janyo wa Najeriya, domin in za ka hana mai bara sai ka ba shi abin da zai ci ya ishe shi. Yaushe gwamnati za ta bai wa masu bara abin da za su ci ya ishe su, tana nan tana fama da ma’aikatanta? Wadansu suna nan ba a iya biyansu albashi a kan lokaci, balle a hana mai bara kuma ba ba shi abinci za ka yi ba. Allah Yana cewa, “Hazihi nakatullahi lakumu aya fazaruha ta’akulu fi ardillah wala tamassuha bisu’i fayakhuzahum azabun karib au azabun alim au azabun azim…” Cikin wannan  aya, Allah Yana cewa taguwa ce ba dan Adam ba, wadda ta zamo mu’ijiza ta Annabi Salihu (AS), Allah Ya gargadi mutanen Annabi Salihu cewa su kyale wannan taguwa ta yi yawo a doron kasa, ta ci ta sha, kada su taba ta. To amma da suka yi taurin kai, Allah Ya hallaka su gaba daya a kan wannan taguwa ta Allah. To, ina masu hana dan Adam Musulmi mai neman Alkur’ani abin da zai ci? A kan taguwa aka halaka mutanen Annabi Salihu, to wai masu maganar nan su ba Musulmi ba ne? Shin ba su karanta Kur’ani ne? To wallahi kada a jawo mana karin fushin Allah. Wallahi aka hana bara ba a tanada musu abin da za su ci ba, masifar da za mu fada a kasar nan abin babu kyau. Su miskinan nan fa Allah Yana sonsu kamar yadda Yake son kowa, ba laifi suka yi wa Allah ba Ya maida su haka. A kiyaye, idan ba haka ba za mu jawo mummunar fitina a kasar nan. Idan kuma an matsa za mu yi addu’a su miskinan nan Allah Ya maida su matsayin masu hana barar, su kuma masu hanawa Allah Ya maida su matsayin miskinan kuma Allah zai amsa don haka a kiyaye.

Yanzu ma muna cikin bala’in yunwa da matsuwa da damuwa a kasa, mun rasa inda za mu sa kanmu saboda rikicin zagin waliyyai da kafirta Musulmi da ake yi ya jawo fushin Allah a kan kasa. Mutane suna karkashe mutane  ba gaira ba dalili, sun hana mu zama lafiya saboda Allah Ya yi fushi ana gaba da waliyyanSa, ana zagin amajiransu ana kafirta Musulmi. Yanzu kuma ana so za a sake jawo mana wani babban bala’i na hana miskinai masu bara, ba a ba su abinci ba. Wannan abin da zai rikito da shi a Najeriya ya fi wanda muke ciki muni. Allah Ya shigar da wata mace wuta a Lahira saboda kyanwa, ta tare ta ba ta ba ta abinci ba, ba ta bar ta ta je ta nema da kanta ba har ta mutu, sai Allah Ya sa matar a wuta.

Shin bara na da asali a Musulunci?

Wa ya ce bara ba ta da asali a Musulunci? An yi bara a gidan Manzon Allah (SAW), ya ce mai barar nan a ba shi abinci, aka ba shi. Sai ya sake jin muryarsa yana bara, ya ce a’a, mai barar nan ba na ce a ba shi abinci ba? Aka ce ya Rasullulahi an ba shi! Ya ce to ku kara masa, Aka kara masa, sai ya sake jin muryarsa yana bara, ya ce mai barar nan ba na ce ku kara masa abinci ba? Aka ce an kara masa ya Rasulullahi. Sai ya ce to ku kyale shi, watakila kudi yake so.

ADVERTISEMENT

To, ka ga Annabi ya bai wa mai bara abinci, ya kara masa; bai hana shi ba. Ya kara yin bara ya ce a bar shi watakila kudi yake so, bai hana shi ba. Da ya hana shi, in da bara ba ta da asali a Musulunci. Annabi bai hana bara ba kuma Allah Ya ce in mai bara ya yi bara kada ka yi masa tsawa, ka yi masa magana mai dadi, je ka gaba Allah Ya ba da sa’a. Magana mai dadi ta fi ka ba shi sadaka ka zage shi, ka ce masu barar nan kun damu mutane kamar kwarkwata.

Allah Ya rasa abin da zai bai wa miskinan ne? A’a, ita ce amsar, amma Allah Ya bar masu bara ne don su zama su ne ’yan dakon kayan da za su kai wa wadanda suke yi wa barar kaya a ranar Lahira, tunda in an je Lahira ba kayansu a can, masu barar nan su ne za su yi musu dakon kayansu na duniya; su kai musu Lahira. Duk wanda ya ba da sadaka yana so ne Allah Ya ninnika masa, Ya biya shi a Lahira. Yanzu a ce an hana motocin dakon mai daukar mai, don Allah motoci za su yi aiki?

Ko akwai wata shawarar da za ka ba gwamnati game da wannan batu?

Ai na riga na gama magana, duk wanda zai hana bara sai ya bai wa mai barar abin da zai ci, in ba ya da ikon ba shi to ya bar shi ya yi bararsa. Idan kuwa ya ki zai gamu da Allah. Wannan ai zalunci ne, dalili in dai bara ta gaskiya ce, ba ta fojare ba; don akwai mutanen da su ba karatu suke yi ba, suka maida kansu masu bara, suna bara tare da almajirai. Wannan bara ce ta fojare, ba a son irin wannan, za ta lalata kasa, ta hana mutane yin aikin raya kasa. Amma bara irin ta Alkur’ani, an gada ne tun zamanin Annabi (SAW). Duk wanda ka ji yana bude baki yana cewa babu bara a Musulunci, to bai san ma Musuluncin ba ne, tun da Annabi (SAW) bakin da suka je wajensa, suka kaura suka koma Madina, su ake kiransu Almuhajirin. To, daga nan aka samu sunan almajiri. Su ma munafukan Madina manya suka yi taro suka ce ya kamata a hana musu abinci, don su bar musu garinsu. Saboda haka almajirai baki ne na Allah, mutum ya haifi ’ya’yansa dole ya kai su su yi karatun addini, dole ya kai su su yi karatun duniya, dole ya bar wadansu su taimaka masa. To shi kansa ba zai iya bin ’ya’yansa da ya kai su makaranta din nan ya kula da abincinsu, ya kula da wajen kwanansu ba. Kuma shi ma mutumin da aka kai masa almajirai ba ya da ikon ya ciyar da ’ya’yansa ma balle ya ciyar da almajiran. Sai aka bar abin a kan gayya na masu aikata aikin alheri su ba su abinci da dare, su ba su abinci duk lokacin da suke bukata. Su kuwa su saurari lada wajen Allah. To amma Nasara shi da bai damu da Lahira ba, ko abincinsa ya saura ba zai bai wa wani ba. Nasara in ya yi bako ba zai saukar da shi gidansa ba sai ya saukar da shi a otel ya biya otel din, har da abinci ma amma ba dai ya saukar da shi a gidansa ya ci abinci a gidansa ba. To haka suke amma mu a wajenmu abin da ka rage ka bai wa almajiri ya ci, ya fi wanda kai ma ka ci a cikinka balle wanda ka mutu ka bari aka gada.

To almajiran Nasara su ke da iko a duk duniya. A yau a duk duniya duk wanda ka gani da iko, in ka bincika almajirin Nasara ne, ko Nasaran Ingilishi ko na Faransa ko na Jamus ko Nasaran ko’ina, su ke da mulki su ke da murya. Sai su daga murya ka ga almajiran boko wadansu suna Amurka, wadansu suna Ingila, wadansu Jamus; ba wanda ya ce komai sai dai wadanda ke zuwa tsakanin gari da gari a cikin kasa a ce ana yawo da almajirai. Akwai wata gwamnatin da aka yi, wani lokaci ba ka da iko ka shiga mota da allo sai a kama ka a ce kai dan Tatsine ne. Sai da muka tashi tsaye muka ce duk wanda ya sake kiran mu masu karatun Alkur’ani da cewa mu ’yan Tatsine ne to za mu yi kararsa.

Shi Tatsine ko duk wani abu da ya zo da tada hankali ra’ayi ne, wanda aka watsa direbobi kuma suka dauka kuma almajiran  wadansu sun dauka su ke yin irin wadannan abubuwa amma hana bara zalunci ne. Almajiran ma ba za ka gan su sun je gidan Minista ko Gwamna ko Sakataren Gwamnati ko Shugaban Karamar Hukuma suna bara ba. Wadanda ake bara a gidansu ba su damu ba, ba su yi kara ba, to me ya dame ka? Ka bari mana bawan Allah ya ci abinci a hannun bayin Allah. Wanda aka hana ya yi bara a Musulunci, shi ne kato mai lafiya, wanda yake da karfin da zai nemi abinci amma miskini da mai neman ilimin Alkur’ani dole ya fita ya nemi abin da zai ci don gwamnatin ba ta ba su ba. Don haka idan ana so a hana bara, to a tanadar wa masu bara abin da za su ci shi ne zaman lafiyarmu, a kiyaye a nema mana zaman lafiya; Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya albarkar Manzon Allah.

Share