Da Dumi Dumi

Hana shigo da abinci kasar nan gata ne ga manoma – Aminu Yahaya

Wani manomi kuma shugaban kasuwar ‘yan tumatur dake garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Aminu Yahaya Yunusa ya bayyana cewa babu shakka matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka, na hana shigo da kayayyakin abinci ta kan iyakokin kasar nan, gata ce take yi wa manoman Najeriyar. Alhaji Aminu Yahaya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya.

 Ya ce hana shigo da abinci zuwa cikin kasar nan, manoma ake yi wa gata. Domin idan aka hana shigo da abinci dole ne a rika sayen abincin da manomanmu na cikin gida suka noma da daraja.

Ya ce a duk ranar da aka ce manoma suna yin noma, suna yin asara saboda karyewar darajar kayayyakin amfanin gonar da suka noma,  za su daina yin noman kamar yadda ya faru a baya, wanda wannan  babbar asara ce ga kasar baki daya.

 “Amma ya kamata manoma su lura duk kayayyakin amfanin gonar da suka noma sun noma ne don a sami sauki. Ba sai kayayyakin amfanin gonar ya yi muguwar tsada ba. Amma in son samu ne idan manomi ya yi noma kada ya yi asara. Idan manoma suna cin riba, ba za a daina yin noma ba, a kasar nan.”

ADVERTISEMENT

 Alhaji Aminu Yahaya ya yi bayanin cewa babu shakka gwamnatin nan   ta lura babu abin da ya fi noma mahimmanci a wajen talakawan Najeriya. Domin shi ne zai iya samarwa da talakawan kasar nan ayyukan yi. Don haka ta tashi tsaye wajen bunkasa harkokin noman.

 Ya ce sakamakon kokarin da wannan gwamnati ta yi, bana mutane da yawa sun rungumi aikin noma a Najeriya kuma bisa dukkan alamu daga bana mutane za su cigaba da aikin noma a Najeriya tukuru. Ya ce wannan ba karamin cigaba ba ne ga al’ummar Najeriya da gwamnati baki daya. Domin da yardar Allah daga wannan shekara tattalin arzikin Najeriya zai farfado sakamakon wannan noma da aka yi. Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta kara sanya ido kan takin zamani a kasar nan, domin a cewarsa idan gwamnati ta yi haka kowa zai koma noma a Nijeriya. 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya