✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hango rashin nasara ne a kotu ya sa PDP ta kidime – APC

Gwamnatin Jihar Kano, ta yi soki Jam’iyyar PDP kan wani kuka da ta fara yi  cewa gwamnati na kokarin sauya alkalan da za su saurari…

Gwamnatin Jihar Kano, ta yi soki Jam’iyyar PDP kan wani kuka da ta fara yi  cewa gwamnati na kokarin sauya alkalan da za su saurari karar shari’ar Gwamnan Jihar a Kotubn Daukaka Kara

Gwamnatin ta musanta zargin da PDP ta yi, inda ta ce PDP na kokarin goga wa alkalan bakin fenti ne kawai.

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce PDP ta kidime, kuma ta rude, tana jin tsoron sake shan kashi a gaban Kotun Daukaka Kara kan zaben jihar,  Malam  Muhammad Garba ya ce  koda an sauya alkalan da za su saurari karar, kotu tana da hurumin zaben alkalanta da za su karbi wani korafi.

Kwamishinan ya ce Jam’iyyar PDP ta yi fice wajen yada karairayi yayin da duk ake gaban kotu.

Kwamishinan ya ce jam’iyyar ta yi irin wannan lokaci da ake shari’ar sauraron korafin zaben Gwamnan Jihar Kano da kuma karar zaben Shugaban Kasa.

Kwamared Garba ya ce “Abin takaici ne a ce jam’iyyar adawar da ta shigar da kara ta hanyar da ta dace a kotu za ta buge da wani zargi da ba shi da makama.”

Ya ce ba laifi ba ne don ’ya’yan Jam’iyyar APC sun nuna gamsuwarsu game da yadda shari’ar ta kaya, a farko amma ’yan takararta ba su da niyyar tsoma baki a cikin shari’a.