✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hankalin mazauna Abuja ya tashi kan yawaitar satar mutane

Hankalin wadansu mazauna Abuja, Babban Birnin Tarayya ya fara tashi sakamakon matsalar satar mutane da ta fara yawaita a birnin. Rahotanni sun nuna cewa akalla…

Hankalin wadansu mazauna Abuja, Babban Birnin Tarayya ya fara tashi sakamakon matsalar satar mutane da ta fara yawaita a birnin.

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum biyar ne aka sace a cikin mako guda a birnin, ciki har da ‘yar wani babban dan siyasa.

Amma an sako ’yar wannan dan siyasa, duk kuwa da cewa wasu rahotanni na cewa sai da aka biya makudan kudi kafin a sako ta.

Matsalar satar mutane ba sabon al’amari ba ne a wasu sassan Najeriya da jihohin da suka yi wa Birnin Tarayyar kawanya.

Wannan matsalar ce ma ta sa mutane da dama, musamman masu sukuni ke kaurace wa hanyar motar daga Abuja zuwa Kaduna, ciki har da manyan jami’an tsaro da manyan ma’aikatan gwamnati.

A yanzu al’umma sun fi aminta da bin jirgin kasa domin sufuri a tsakanin manyan biranen biyu masu makwabtaka da juna.

Sai dai a dan tsakanin nan matsalar satar mutanen ta kunno-kai a Babban Birnin Tarayyar, har ta kai ga wasu unguwanni na masu hali.

A birnin na Abuja, akwai lokacin da aka girke kyamarorin tsaro a bangarori daban-daban na birnin.

An yi haka ne don inganta tsaro, amma bincike ya nuna cewa mafi yawan wadannan kyamarori sun bace.

Sai dai Rundunar ’Yan sandan Najeriya, a wata sanarwar da ta aike wa gidan rediyon BBC, ta bayyana cewa ana azizita tabarbarewar tsaro a Abuja da yawaitar satar mutanen, amma lamarin bai kai yadda ake fada ba.