✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hankalinka Jagoranka

Barin sallama kan saduwa ko gamuwa a kan hanya:   26 Ba a sallama wa budurwa wadda ba muharramarka ba, ko ita ajanaba in akwai…

Barin sallama kan saduwa ko gamuwa a kan hanya:

 

26 Ba a sallama wa budurwa wadda ba muharramarka ba, ko ita ajanaba in akwai aure tsakaninku yankakke a kan hanya.

27 Ba a sallama wa budurwa ajanaba da nufin aure ba da izinin iyayenta ba, domin kasancewarta manisanciya.

28 Ba a sallama wa bazawara cikin idda da nufin aure balle nema, amma ana iya daura auren ta da ta kare, tare da nema da yin magana, a ranar a lokaci daya.

29 Ba a son sallama da budurwa balle wani abin da zai biyo bayan sallamar, amma ba a hana sallama ga tsohuwa ba, ko a kan hanya.

30 Ba a amsa sallama ga wanda ko wadanda ba a yarda a yi masa sallama ba, sai dai ta al’ada ko a ce a kanku, ga masu tarbiyya.

31 Ba a sallama ga masu wasa ko masu saba wa Allah, ko dabbobi da wadanda aka san ba za su amsa ba, sai don sanayya.

32 Ba a hana yin sallama ga wanda ba a san halinsa ko addininsa ba, domin shi ko su za su san ka koda a kan hanya.

33 Ba a sanin addinin mutum in ya gamu da wani ko wadansu don sutura ko magana sai don sallama; ko a kan hanya.

34 Ba a sanin kai Musulmi ne ko ba Musulmi ba, sai in ka yi sallama, haka kai ma ba za ka san masayonka ne ba ko makiya.

35 Ba a barin sallama yinta ne ko amsata, a kan haduwa ko gamuwa da wanda ma ba ka sani ba, ko a kan hanya.

Barin sallama kan haduwa ko gamuwa a hanya, sai ga wanda aka sani, yana sanya kin  dan uwa da daidaita su ko shi ko ita da makiya