✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hankalinka Jagoranka

Mahmud Sabo Wushishi   Kade-kade  da raye-raye da wake-wake da tallace-tallacen manya da yara   96 Kade-kade da wake-wake da raye-raye da tallace-tallace, ga yara…

Mahmud Sabo Wushishi

 

Kade-kade  da raye-raye da wake-wake da tallace-tallacen manya da yara

 

96 Kade-kade da wake-wake da raye-raye da tallace-tallace, ga yara da manya, abubuwa ne masu wuyar hanawa ko bari, a birane da kauyuka, saboda talaucin da ke tare da mutuwar zuci da jahilci da al’ada ta mu’amalar manya da yara.

 

97 Kadi da tariya da tankade da rairaya da bakace da barji da markade da sussuka da shukawa da dasawa da girbewa da sarawa da kushere da kohi da sassabe da yafe da yanta da zana da boto da tanka da yabe da gini da yiwo itace da sayar da itace da baibaye da sassaka da saka da sara.

Kadan ne cikin sana’o’i Arewa da dan Bahaushe, ban da wadanda ake ta gado da noma da kiwo wanzanci da kasuwanci da fawa da su da masunta da mafarauta da masu koyarwa da malamai na gida da na gwamnati da masaka da teloli da direbobi ko ’yan dako ga makera.

 

98. Kade-kade da maraya da mawaka da mabusa, sarakai da ’yan kwangila da masu fatauci da ’yan sufuri da ’yan kamasho da ’yan kwal da ’yan dambe da kokawa da masu barkwanci da ’yan tauri da masu shela da ’yan kwantai da dillalai da masu busa duk sana’o’i ne.

 

99. Karatu da yin ilimi da aiki da ilimi da kawar da girman kai wurin sana’a da barin mummunan zato abubuwa ne da za su sa mutum ya yi mutunci.

100. Ka nemi abin yi na halaliya ba sai gwamnati ta samar maka ba, ina mutuncin mutum babu aikin yi, balle dalibi ko malami kuma na bara?

Za a iya samun Malam Mahmud Sabo Wushishi ta: 08055736329,

08034358678