Da Dumi Dumi

Hannun da tallafin noman citta ke biyowa ba nagari ba ne – Auwal Abubakar

Aminiya: Me da me kake nomawa?

Ina noma hekta daya zuwa biyu na masara sai kuma citta nakan noma hekta biyu zuwa uku.

Aminiya: Akalla me da me ake bukata don noman citta?

Farkon abin da manomi kowane iri ne ke nema shi ne jari. Da jarin ne zai nemi sauran abubuwan da suka hada da takin zamani da na gargajiya. Bayan su kuma akwai kayayyakin kaftu na zamani wanda su suka fi sauki ga manomin citta. Misali akwai wani inji na zamani ana kiransa Power Tiller, wata tarakta ce ta hannu wanda ake tura ta, in manomi ya same ta zai samu saukin aiki musamman mu nan kusan leburori kawai muke yi wa aiki duk da dai ba za mu fasa ba.

Aminiya: Masu sayen citta a bana suna kuka a kan yawan kwari a busasshiyar citta, me ya kawo haka?

ADVERTISEMENT

To kwari iri-iri ne, akwai kwarin kafin shuka akwai na bayan shuka wadanda ake samu a busasshiyar citta bayan girbi. Su na farkon da ake yi kafin shuka dama suna rayuwa ne a jikin cittar wadanda akasarin manoman ba sa gane su saboda za ka gan su fari-fari ne kamar yana, ba su san cewa su ne kwayayensu ba. Abin da ke kawo su kuma shi ne rashin gyara citta. Yanayin yadda ake ajiye iri kafin shuka ya kamata ya zama an yi masa feshi tukuna.

Su kuma kwarin da ake samunsu a busasshiyar citta bayan ajiya suna zuwa ne saboda rashin samun isasshiyar rana yayin busar da ita. Yawancin manoma suna so a ce cittarsu ta yi nauyi wanda shi ne ribarsu tunda aunawa ake yi a sikeli, to sai ba sa bari ta bushe sosai don ta kara nauyi. idan akwai danshi a jikinta. Wannan da kuma sauran wasu dalilai a ganina su ke kawo ka ga kwari sun yi yawa a jikin citta.

Aminiya: Ga mai son fara noman citta wane lokaci ya kamata ya shuka ta?

Idan har an samu damina ta fara da wuri to daga karshen watan uku (Maris) zuwa farkon watan hudu (Afrilu) ne daidai lokacin sa citta, insha Allahu za ta yi kyau idan an samu ruwa sosai. Amma idan mutum ya makara to zai iya sawa a tsakiyar watan hudu zuwa tsakiyar watan biyar har zuwa karshensa. Sai dai kamar kasar Kagarko da kasar Jaba su suna sa wa har a watan shida don su bar ta ta shekara a kasa.

Aminiya: Bayan shuka citta wace dawainiya take bukata?

Akalla dai citta tana son a bar ta a kasa kamar zuwa wata bakwai. Citta ba ta son zama a cikin ciyawa domin in an bar ta, ba za ta yi kyau ba, don haka tana son a rika cire ciyayi a cikinta in dai ana son ta yi ’ya’ya da yawa. Sannan sai fesa magungunan kashe ciyayi wadanda ba za su lalata cittar ba. Sai dai wata matsala da muka fahimta ita ce idan mun yi amfani da irin wadannan magunguna to in shekara ta kewayo kuma ba za mu sake ganin irin maganin ba kusan haka yake faruwa kowace shekara. Duk da mu ma muna da irin tamu fahimtar na hade-haden wasu abubuwa don kashe ciyawa amma su bar cittar, to sai dai akwai hadari domin in aka samu akasi zai iya lalata cittar gaba daya tunda ba wasu gwaje-gwaje masana suka yi a kai ba.

Aminiya: Yaya za ka kwatanta daminar bana da ta bara?

Daminar bana gaskiya ta yi kyau. Mu kan ji wadansu na cewa daminar bara an fi ruwa, to amma muna jin su ne kawai, domin daminar bara an fi manyan ruwa ne amma na bana ya fi. Domin ruwan bana shi ne wanda kowane irin amfanin gona ke son irinsa na marka-marka sai dai wanda ba a sa masa taki ba ko kuma yana da karancin albarkar kasa.

Aminiya: Kuna da wata lema ce da ta hada manoman citta?

Eh, muna da ita a nan karamar Hukumar Jama’a sai dai kusan da ita da babu duk daya ne, domin ba ta amfana wa manoman komai. Abin da yake faruwa shi ne wadansu tsofaffin manoma ne wadanda yanzu ba noman suke yi ba su suka hada kai da shugabannin Sashen Noma na karamar Hukumar suna karkatar da duk wani tallafi ko taimako da ya kamata ya fada hannun manoma. Wadanda tallafin ke zuwa ta hannunsu suna kashe-mu-raba ne kawai tunda yawancinsu, in ma ba dukansu ba, ba noma suke yi ba sai dai a kwashe kayan a je a sayar wa ’yan kasuwa, manoma kuma a bar su a tutar babu,su je kasuwa su saya. Misalai manoman da ke cikin garin Kafanchan dukanmu mun san kanmu da wadanda ke cikin kungiya da wadanda ba su shiga ba duk mun san juna, amma cikin kashi dari na manoman cikin gari babu mutum daya da ya amfana da wani tallafi sai mutum daya ya san kansa, shi kuma ba yana kishin manoman ba ne sai dai kansa kawai.

Aminiya: Mene ne kiranka ga gwamnati?

Kiran da zan yi wa gwamnati shi ne wurin tallafa wa manoman citta da farko mun yi murna da irin kudirorin da gwamnati ke da su na tallafa wa manoma, to amma matsalar da aka samu ita ce hannun da tallafin ke biyowa ba hannu nagari ba ne. Bilhasali ma za mu iya cewa masu son yi wa wannan gwamnati kutunguila ne kan kokarinta na tallafa wa harkar noma su kuma suke kokarin tadiye mata kafa ta bayan fage. Abin da ya sa na ce haka shi ne abin ba ya zuwa hannun manoma na gaskiya da aka san su kuma aka san gonakinsu.

Da a ce gwamnati za ta tallafa wa manoman citta da kayyayyakin aiki cikin sauki da manomi zai ci riba sosai, ba ya zama leburori ne kawai ke cin gajiyar noma ba. Misali injin da na bayyana maka a baya da magungunan feshi na kwari da takin zamani da sauransu to da mun yi farin ciki sosai.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya