✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyar da aka gano ’ya’yanmu da aka sace – Iyayen Yaran Gombe

A ranar 20 ga Oktoban da ta gabata ce, wani karamin yaro mai suna Musthapha dan kimanin wata 21 yana wasa da yayyensa a tsakar gidansu…

A ranar 20 ga Oktoban da ta gabata ce, wani karamin yaro mai suna Musthapha dan kimanin wata 21 yana wasa da yayyensa a tsakar gidansu da ke Unguwar Kagarawal a garin Gombe da misalin karfe biyar na yamma sai wadansu mata da ba a sansu ba suka shiga gidan cikin sirri suka sace shi.

A lokacin da aka sace yaron, mahaifinsa Abdul’aziz Suleiman yana shagonsa a Babbar Kasuwar Gombe yana harkokinsa, kawai sai ya ji kira daga matarsa Maryam, inda ta sanar masa cewa dansu na biyu Musthapha ya bata.

Suleiman ya shiga rudu, inda nan take ya rufe shagonsa, ya nufi gida ya hadu da wadansu makwabtansa da ’yan uwa suka shiga neman Mustapha a gidajen makwabta da kuma unguwar amma ba su same shi ba.

A lokacin da suka kai rahoto ga ofishin ’yan sanda washegari, ashe lokacin wadanda suka sace yaron sun kama hanyar zuwa Jihar Anambra da shi, inda suka kai shi suka sayar a kan Naira dubu 750.

Bayan bacewarsa, Musthapha ya shafe mako guda a hannun wadanda suka sace shi, kafin ’yan sanda a Jihar Anambra su ceto shi daga hannun wadansu mata uku da ake zargin su suka sace shi daga Gombe suka kai shi Anambra don sayarwa.

Mahaifiyarsa Maryam ta shaida wa wakilinmu yadda aka yi aka sace mata da da kuma yadda ta ji a wannan ranar. Ta ce tana aikin dafa abincin dare a kicin, ba ta ankara ba ya sulale ya fita waje, ya samu yara suna wasa a tsakar gida.

“A lokacin da yayansa ya dawo gida daga Makarantar Islamiyya, shi ne nake tambayarsa ina kanensa, ya zo su ci abinci. A nan ne ya gaya min cewa bai gan shi ba. Sai na kira mahaifinsa na sanar da shi abin da ya faru. Daga nan muka sanar da dagacinmu, wanda ya tura jama’a su fara nemo shi a unguwar. Ba a same shi ba, sai muka sanar da ’yan sanda,” inji ta.

Shi ma mahaifin yaron ya bayyana cewa bayan sun yi cigiya tsawon mako guda ba su samu dan nasu ba, sai suka hakura suka mika komai ga Allah. Suka dukufa ga addu’o’i.

“Ranar wata Asabar da ta wuce, wani abokina ya nuna mini hoton wadansu yara biyu da suka bace, ’yan sanda suka same su a Jihar Anambra. Da Allah Ya taimake ni, ina dubawa sai na gane daya daga cikinsu kuma dana ne da aka sace. Kuma tunda aka sace shi, mahaifiyarsa ba ta iya barci,” inji shi.

Wani abin takaici a wannan rana da iyayen Musthapha suke jimamin bacewar dansu, sai wani mai suna Yusuf Musa da ke Unguwar Riyal Gombe shi ma matarsa Fatima ta kira shi, ta gaya masa cewa dansu mai shekara uku mai suna Musa (Walid) ya bace, ba a gan shi ba.

“Matata ta sanar da ni cewa Walid yana wasa ne a waje da kannensa, kawai sai muka neme shi muka rasa. Mun duba gidajen makwabta duka ba mu gan shi ba. Sai muka hanzarta zuwa ofishin ’yan sanda na Unguwar Pantami, muka ba da rahoton bacewarsa.

Bayan mako daya da batarsa, muna ta addu’o’i, sai wani ya karanta a jarida cewa ’yan sanda a Jihar Anambra sun samu yara biyu da aka sato daga Gombe, aka kai su Anambra. Sai ya sanar da makwabcina, wanda ya gane Walid, daga bisani ni tare da mahaifiyarsa muka tabbatar da danmu ne da ya bace,” inji shi.

Yusuf ya kara da cewa sai suka hallara a ofishin ’yan sanda na Pantami, inda aka shirya daukarsu domin zuwa Jihar Anambra don ganawa da ’ya’yansu.

A cewarsa, sun ga yara da dama a gidan marayu, inda aka kai yaransu aka ajiye. “Wani abin mamaki shi ne, mafi yawancin yaran suna da kama irin ta ’yan Arewa,” inji shi.

Fatima Ahmed, mahaifiyar Walid, ta ce ta yi matukar kaduwa tsawon mako guda da rasa danta amma ta ce “Ba ku ji yadda na ji ba a lokacin da na rungumi dana a harabar hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra.”

Wakilinmu ya gano cewa kafin ’yan sanda a Jihar Anambra su ceto wadannan yara har an sanya kudin sayar da Musthapha a kan Naira dubu 750, shi kuma Walid an yi masa kudi Naira dubu 850, ga duk mai bukatar sayensu a lokacin.

Hauwa Usman, daya daga cikin wadanda ake zargi da sace yaran, wadda ta ce ita ce mahaifiyar daya daga cikin yaran kuma a cewarta dayan dan yayarta ce da ta rasu ta bar ta da shi.

Sai dai wani rashin sa’a da masu satar yaran suka yi shi ne ya sa Allah Ya kawo ’yan sanda a Jihar Anambra suka ceci yaran daga hannunsu.

’Yan sandan sun ce yaran da suka kubutar din sun kai su sashin kula da walwala na ofishinsu, kafin nemo inda iyayensu suke.

Mai magana da yawun ’yan sandan Gombe, Hauwa Mohammed ta ce yaran an ba da su ga wadanda suka zo suka tabbatar da cewa ’ya’yansu ne, bayan gudanar da binciken da ya tabbatar su ne iyayen nasu na hakika.

A cewarta, wadanda ake zargin su ne Faith Okpai, mai shekara 38, ’yar asalin Jihar Kuros Riba da Ngozi Elisiobi mai shekara 52, ’yar asalin Jihar Anambra  sai  Hauwa Usman mai shekara 24, ’yar asalin Jihar Gombe.

Tuni aka tura su hedkwatar ’yan sanda na Jihar Gombe domin ci gaba da binciken a kan lamarin. A ranar Alhamis din makon jiya ne hedkwatar ’yan sandan Jihar Gombe ta mika yarar da aka ceto ga iyayensu.

Da yake magana da wakilinmu bayan mika yaran, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da bangaren mulki, Mista Aled Wanang ya ce jami’ansu a Jihar Anambra ne suka ceto su ta hanyar rahotannin sirri.

Ya ce babbar wadda ake zargi, Hauwa da ta ce sunanta Blessing John da take tare da sauran wadanda ake zargi su biyu, dukkansu suna hedkwatar ’yan sandan Jihar Gombe yanzu haka don gudanar da bincike a kansu.

Da suke amsa tambayoyin wakilinmu, matan uku da ake zargi da sace yaran, Hauwa da Elisiobi da Okpai, kan yadda suka samu yaran har suka tafi da su Anambra, sun musunta cewa su san an yi wa yaran kudi Naira dubu 750 da 850. Hauwa ta ce Okpai ce ta sato yaran ta nemi ta raka ta da su zuwa Jihar Anambra domin ta sayar da su. Faith Okpai kuma cewa ta yi Hauwa ce ta kawo mata yaran, ba ita ta kamo su ba.

Sannan Ngozi ta bayyana cewa ita ba ta  taba ganin Hauwa da Faith da idonta ba, yanzu ta fara ganinsu a karon farko a hedkwatar ’yan sandan Anambra.