✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi biyar da za mu bi domin inganta fatar jikinmu

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Yana da kyau mace ta kasance mai yawan kintsi da gyara…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Yana da kyau mace ta kasance mai yawan kintsi da gyara jiki a koyaushe. Musamman in  ta kasance matar aure ce. Sau da yawa sai a ga mace daga ta haihu daya  ta fita kammaninta. Idan mace ta kasance  mai yawan kintsi, a kullum maigida zai rika yi mata kallon budurwa. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin inganta fatar jikinmu.

• Idan ana so fatar jiki ta kasance da sulbi a kullum, za a iya hada man zaitun da gishirin teku (sea salt); za a iya samun wannan gishirin a manyan shagunan da ake sayar da kayan kwalliya. Idan aka kwaba su sai a rika dirzawa a jiki a kullum kafin a shiga wanka. Yin haka na cire matacciyar fatar da ke jiki kuma ya fitar da sabo. Bayan haka, ga sanya fata sulbi da laushi.

• Idan ana yawan shafe-shafe, kuma fatar ta yi wani dabbare-dabbare, sai a samu lemun zaki ko na tsami ana goge inda wannan fatar ta canja launi. Sai a jira na tsawon minti hudu sannan a wanke. Yin haka na haskaka wannan wurin da ya kode a fatar.

• Man tuffa na daya daga cikin abubuwan da ke gyara fatar kai. Kuma yana warkar da kowace irin cuta ta fatar kai. A samu man tuffa kamar kofi daya sai a hada da ruwa sannan a wanke kan da shi duk lokacin da kan ya yi dauda. Yawan amfani da man tuffa na rage fitowar amosanin ka da  kurajen ka.

• Zuma za a same ta a ko’ina. Tana dauke da sinadarai da dama kamar na sanya sulbin fata da kuma warkar da tabo da sauransu. A shafa zuma a fuska a kullum kafin a shiga wanka, sannan a bari ta dan jima na minti goma sha hudu sannan a wanke da ruwan dumi. Yin haka na warkar da kurajen fuska da sanya ta haske da sulbi.

• A kasance ana da man kwakwa a kullum domin wannan mai na gyara fatar kai da kuma sanya gashi laushi da santsi da kuma tsawo. A shafa man kwakwa a fatar kai sannan a rufe kan da leda. Bayan awa daya sai a wanke za a yi mamaki.