✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi mafiya sauki da za a inganta kwalliya

To manyan mata! Idan na ce manyan mata ina nufin wadanda suka dan kwana biyu a  gidan aure. Kada ku bari yara kanana su sace…

To manyan mata! Idan na ce manyan mata ina nufin wadanda suka dan kwana biyu a  gidan aure. Kada ku bari yara kanana su sace zukatan mazanku da wani kyalkyal-banza. Gyara ga mace dole ne da zarar tana son faranta wa maigidanta rai. Don haka, kada a bari sha’anin yara ya sanya a zamo kamar an tsufa. A dage da gwada irin yadda mace za ta kintsa kanta a shafukanmu na kwalliya da muke kawo muku a kowane mako domin inganta kwalliyar gashi da fata da sauransu.

• Idan ana fama da rashin shekin gashi, sai a sayi kwayar ‘aspirin’ daya  a nika ta a zuba a cikin nau’o’in man wanke gashi a kwaba sosai su kwabu sannan a rika wanke gashin kai da shi bayan kowane mako biyu za a ga canji.

• ’Yan matan yanzu sun dage da gyaran gida. Duk da cewa akwai haramci wajen aske gira, akwai dabarar da uwargida za ta iya yi wajen zana girarta ya dan yi kyau tare da shafa hodar kan girar ta yadda za ta nuna sauran gashin kamar a aske ne amma hodar za ta boye su sannan ta maka gazal launin gashin girarta ba launin gashin kanta ba.

•Yawan sanya ruwa a gashi na matukar karya gashi. Idan an kasance ana yawan sanya ruwa a gashi, sai a kwaba fiya da man zaitun a rika shafawa a fatar gashin kai na tsawon minti goma a kullum kafin a wanke. Yana rage karyewar gashi.