Da Dumi Dumi

Hanyoyi mafiya sauki da za a inganta kwalliya

To manyan mata! Idan na ce manyan mata ina nufin uwayengida da amare waDanda suka Dan kwan biyu a gidan aure. Kada ku bari yara kanana su sace zukatan mazanku da kyal-kyal banza. Gyara ga mace dole ne, matukar tana son faranta wa maigidanta rai. Don haka, kada a bari sha’anin yara ya sa a zamo kamar an tsufa. A dage da gwada yadda mace za ta kintsa kanta a shafukanmu na kwalliya da muke kawo muku a kowane mako domin inganta kwalliyar gashi da fata da sauransu.

Idan ana fama da rashin shekin gashi, sai a sayi kwayar ‘aspirin’ Daya a nika ta a zuba a cikin man wanke gashi a kwaBa sosai su kwaBu sannan a rika wanke gashin kai da haDin bayan kowane mako biyu za a ga canji.

’Yan matan yanzu sun dage da gyaran gira. Duk da cewa akwai haramci wajen aske gira, akwai dabarar da uwargida za ta iya yi wajen zana girarta ta Dan yi kyau tare da shafa hodar kan girar ta yadda za ta nuna sauran gashin kamar a aske ne amma hodar za ta Boye shi sannan ta maka gazal launin gashin girarta ba launin gashin kanta ba.

•   Yawan sanya ruwa a gashi na matukar karya gashi. Idan ana yawan sanya ruwa a gashi, sai a kwaBa fiya da man zaitun a rika shafawa a fatar gashin kai na tsawon minti goma a kullum kafin a wanke. Yana rage karyewar gashi.

• Kasancewar shekaru sun Dan ja, za a ga waDansu mata kasan idanunsu sun Dan zazzago, yana da kyau a rika a jiye koren shayi sannan a sanya a gidan sanyi sai a rika Dorawa a kan fatar da ke zazzagowar hakan zai sanya ya yi sauki.

ADVERTISEMENT

• Dole ne mace ta kasance da na’urar busar da gashi. Domin duk yadda aka goge shi da tawul ba zai bushe ba kuma hakan na sanya warin gashi.

•   A rika shafa man kwakwa domin sanya fatar jiki laushi da sheki.

Share