✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi mafiya sauki na rabuwa da amosanin kai

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata.…

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wadansu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana mata! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsala ta amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemun tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangwaro.

Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To ga yadda za a sarrafa shi.  

• A wanke ganyen kashu sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa.

• Bayan haka, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon mako biyu insha Allah za a samu saukin amosanin ka.

Ko kun san cewa lemun tsami ma yana warkar da amosanin ka, musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa?

• A samu lemun tsami sai a matse ruwan, sannan a hada da ruwan kwakwa.

• Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke.

Kwallon mangwaro na mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madarar ‘butter milk’ kamar haka;

• A busar da kwallon mangwaro, bayan ya bushe, sannan a daka.

• Za a iya kwaba garin kwallon mangwaro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madarar ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai. Bayan minti 30 sai a wanke. Ana yi a kai-a-kai domin harkar fata sai a hankali ake samun sauki.