Search
Subscribe
Hanyoyin da za a bi domin samun fata kamammiya

Yadda ake shafa haxin gurji

Hanyoyin da za a bi domin samun fata kamammiya

Assalamu alaikum mata. Tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. Za a ga mata suna tsufa da wuri sakamakon yawan haihuwa. Hakan kan sanya fatar jikinsu ta yi yaushi, domin fatar ta wahala don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki da za a bi domin samun fata kamammiya.

 • Gurji: A yawaita cin gurji domin samun fata kamammiya kuma yana hana samun gautsin fata. Za a iya markada shi sai a yi ta shan ruwansa ko a rika yankawa a abinci.
 • Man Castor: Wannan mai na da matukar muhimmanci ga fata domin yana magance cuttutukan da suka shafi fata. Za a iya a wanke fuska da sabulu sannan a shafa man a fuskar a kwanta barci. Kyansa shi a rika amfani da shi sau biyu a rana; safe da yamma.
 • Koren ganyen shayi: Wannan irin ganyen shayi na taimakawa a jiki sosai domin yakan rage kibar tumbi. Bayan haka yana taimaka wa fata ta kame.
 • Ayaba: Tana dauke da sinadarin iron don haka yana taimaka wa fata kamewa. A samu ayaba sannan a kwaba ta sai a shafa a fuska da wuya na tsawon minti ashirin sannan a wanke da ruwan dumi sau biyu a rana.
 • Madara/Kindirmo: Yana taimakawa wajen sanya fata sheki da kuma kame ta. A yawaita shan madara ko a rika shafawa a fuska domin sanya fata sheki da kamewa.
 • Kwai: Za a iya cire kwaiduwar kwai sannan a shafa farin ruwan a fuska a kullum sau biyu, safe da yamma domin samun kamammiyar fata.
 • Gwanda:Tana dauke da sinadarin papain kuma yana taimakawa wajen kame fata idan ana amfani da shi a fuska ko cinsa akalla sau daya a mako.
 • facebook
 • twitter
 • whatsapp
 • linkedin