✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin Kariya Daga Cututtukan Yanayin Hunturu

Wadanne hanyoyi ne mutum zai bi ya kare kansa daga illolin yanayin sanyi kamar su mura da tari? Daga Nasir Adamu Kainuwa da Abba Babba…

Wadanne hanyoyi ne mutum zai bi ya kare kansa daga illolin yanayin sanyi kamar su mura da tari?

Daga Nasir Adamu Kainuwa da Abba Babba da Muhammad M.K

 

Amsa: Akwai bambancin halitta a tsakanin ’yan Adam ta yadda jikin kowa ke karbar yanayi daban-daban. Akwai mutanen da jikinsu ya fi son yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda jikinsu ya fi son yanayi na zafi. A likitance dai akwai muhawarori da za a iya yi dangane da kowane yanayi ne ya fi, dangame da lafiyar al’umma. Amma dai yawan cututtukan da muka fi gani a asibitoci masu saurin kisa irin su ciwon amai da gudawa da kyanda da na zazzabin cizon sauro da zazzabin tafot sukan ragu ainun a lokutan sanyi.

Wannan ya samo asali ne saboda a cikin halittu na kwayoyin cuta, akwai wadanda suka fi yaduwa a yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda suka fi yaduwa a yanayi na zafi. Wadanda suke saka wadancan cututtuka masu saurin kisa, a mafi yawan lokuta sun fi yaduwa a yanayi na zafi. Wasu nau’uka na kwayoyin birus kadai ne suka fi son yanayi na sanyi. Saboda wannan ne ma a kasashe masu sanyi sosai sai an yi wa mutane da dama alluran riga-kafin wasu cututtukan birus don kiyaye mura.

Cututtukan da akan samu lokutan sanyi sun hada da:

Mura: Kwayoyin cutar da kan sa mura duka na birus ne, wadanda suka fi yaduwa a wannan yanayi. Wasu masanan kuma suka ce a’a wadannan kwayoyin suna nan a kowane lokaci amma sun fi yaduwa ne a lokacin sanyi saboda kusancin da muke da juna, da kukkulle tagogi da muke yi, wanda hakan kan sa iska ta kasa kwashe su.

Hanyoyin da za ka bi ka kare kanka daga kamuwa da mura sun hada da barin kusantar mai mura, wato yin nesa da shi. Idan kuma ta kama mutum, zai fi kyau shi mai murar ya bar shiga mutane na tsawon kwanaki akalla biyu, idan kuma ya zama dole ya fita ya shiga mutane, to ya rika yawan amfani da hankici idan zai yi atishawa don kada ya yada wa wasu. Sai kuma yawan wanke hannaye; kowane mutum ya yi musabiha da mai mura dole ya wanke hannayensa da sabulu don kada ya dauki kwayoyin cutar ya baza su. Sai kuma shan ’ya’yan itatuwa a kullum kamar su lemon zaki da na tsami da tanjirin masu sinadaran bitamin C mai kara kaifin garkuwar jiki, su ma za su kare mutum daga mura. Mai murar ya rika yawan shan ruwa da shan abu mai yaji kamar farfesu, don akwai hujja cewa kwayoyin cutar ba su son yaji.

Tari: Ban da mura, lokacin sanyi akan yi tari iri-iri, tun daga tarin mura, wanda ya fi kama tsofaffi da yara zuwa irin su tarin asma da sauransu. Wani tari da ya fi kamari a irin wannan lokaci shi ne wani ciwon tari a yara ’yan kasa da shekara biyar mai fito, wanda ake kira croup a turance, me kama da tarin shika, wanda kansa makogwaronsu ya kumbura, su kasa cin abinci sosai. Za a ji yaro yana numfashi kamar mai asma, numfashi na fitowa kamar ana hura usur, kirji na shigewa ciki idan yana jan numfashin. Idan aka ji irin wannan, dole a kai yaro asibiti domin karbar magungunan sha da na shaka.

Haka nana irin wannan yanayi a karon farko aka fi sanin mutum na da tarin asma, kuma a irin wannan yanayi ciwon ya fi tashi ga mai shi, saboda kurar hazo. Mai asma dole ya rika sa kyalle ko takunkumi mai rufe fuska ke nan a ranakun da ake hazo, kuma ya rika yawo da maganin shaka watoinhaler.

Ke nan ba kamar mura ba, dole a kai mai tari asibiti don a duba shi sosai a ga dalilin tarin a ba shi magani.

 

Sauran halin da jiki kan samu kansa a yanayin sanyi sun hada da:

Ciwon hakori: A mafi yawan lokaci mataccen hakori baya tashi ciwo sai a lokacin sanyi. Wato ba sanyin ne ke jawo ciwon hakorin ba, a’a dama can kwayar cuta ta ci ta cinye har jijiyar karkashin hakorin ta fito. To da sanyi ya tabo wannan jijiya sai fa ya fara ciwo, a wasu lokuta har ya sa fuska ta kumbura. Yadda za a kiyaye rarakewar hakora dai ita ce ta yawan wanke su safe da dare ba safe kadai ba, da yin amfani da ruwan wanke baki na mouthwash mai karfi jefi-jefi da yawan zuwa wanke hakoran.

Idan hakori ya riga ya rarake kuwa ana zuwa a cike ramin hakorin, ko ma a cire shi hakorin gaba-daya.

Sabar fata: Wasu kuma a irin wannan yanayi fitowar fatarsu takan zama sai an gane, wato sai sun yi saba. Masu yawan tambaya a kan cewa suna da wannan matsala a irin wannan yanayi, su kwantar da hankalinsu, su rika yawan shafa mai, don fatar ta yi taushi.

Yawan fitsari:  Shi ma yawan fitsari a irin wannan yanayi hanya ce da jiki ke samu domin fitar da ruwan da ba ya bukata a wannan lokaci na sanyi. Wato in dai ba dama can mutum yana da yawan fitsari ba a lokacin zafi, to kusan yawan fitsari lokacin sanyi alama ce ma ta lafiyar koda. Amma kuma duk da haka ana so mutum ya ci gaba da shan ruwansa daidai wa daida, hakan kan taimaka wa ciki da hanji narkar da abinci. Domin ba abin mamaki ba ne mutum ya ji ya fara samun taurin bayan gida a lokacin sanyi, idan baya shan ruwa sosai. Idan aka ji irin wannan, a ci kayan itatuwa da ganyaye da motsa jiki sosai don bayan gida ya yi laushi sosai

Bugun zuciya: Masu ciwon zuciya iri daban-daban sun fi samun matsaloli a irin wannan yanayi domin ciwon kirji na masu ciwon zuciya da kuma bugawar zuciyar ya fi aukuwa. Wannan na faruwa ne musamman a tsofaffi wadanda jikinsu ba ya samar da dumi sosai, don haka jininsu kan fara daskarewa har zuciya ta tabu. Wato dai dole ne tsofaffi da masu ciwon zuciya su kasance a wuri mai dumi a irin wannan yanayi.

 

Mene ne amfanin lemon tsami ga jiki ne?

Daga Hassan Usman Bebeji

Amsa: Lemon tsami shi ne dan itace da ya fi kowane yawan sinadarin bitamin C mai kara kaifin garkuwar jiki da tsane maikon jiki

 

Rufe gilas ruf a mota da mutum mai wata cuta na da wata illa?

Daga Musa GGC, Kano

Amsa: E, amma sai idan ciwon nasa zai yada shi ne ta hanyar numfashi kamar mura da tari.