✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin magance Satar Zati

Daga bayanan da suka gabata, za mu ga cewa galibin mutane suna zabar “Password” ne ba tare da la’akari da tsaro ba, ko muhimmancin samun…

Daga bayanan da suka gabata, za mu ga cewa galibin mutane suna zabar “Password” ne ba tare da la’akari da tsaro ba, ko muhimmancin samun “Password” mai tsauri ba. Babban dalili shi ne, tunda dole ne sai da “Password” ake iya shiga shafi ko samun riskar nau’in bayanan da ake so, shi ya sa mutane ke kaffa-kaffa wajen zabar abin da yake mai sauki gare su. A halin yanzu ga bayani kan ka’idojin da ke dauke da siffofin “Password” musamman a wannan zamani da muke ciki. Abin da wannan ke nufi shi ne, wadannan su ne ka’idojin da ake son ka bi wajen zabar “Password” dinka a kowane lokaci.

ka’idoji da Siffofin “Password”

Saboda matsaloli da aka yi ta samu a baya, tun bayyanar tsarin “Password” zuwa yau, duniyar fannin sadarwa ta yi wa kanta kiyamullaili, inda ta fara neman hanyar kariya daga sake aukuwar abubuwan da suka auku a baya. A cikin doguwar kasidar da muka gabatar mai shafuffuka 35, kuma mai: “ka’idojin Mu’amala da “Password,” mai karatu ya ga irin badakalar da ta yi ta faruwa a baya, a sashe mai taken: “Tarihin Sace-sacen “Password” a Duniya.” A takaice dai, a halin yanzu an bullo da wasu ka’idoji da dukan hukumomi da kamfanoni a duniya ke bi wajen tsarawa da kintsa bayanansu, daga ciki har da ka’idojin zabar adireshin Imel da “Password.” Wannan ka’ida ita ake kira: “Password Policy,” wadda ka’ida ce da ke karkashin “Email Policy.”

Dukan kamfanonin sadarwa na duniya da ke bai wa mutane damar bude shafi ta hanyar Suna (username) da Kalmar izinin shiga (“Password”) a yau suna da ka’idoji na musamman da suke amfani da su wajen yin hakan. Wasu ka’idojin suna da tsauri, wasu kuma masu sauki ne. Wadannan ka’idoji, wadanda ke karkashin tsarin “Email Policy” ne, wato ka’idojin tsarawa, da bayarwa, da adanawa da kuma lura da bayanan da suka shafi harkar Imel na kamfanin ke nan.  Wadannan tsare-tsare suna taimaka wa kamfanin ne wajen tantance jama’ar da yake hulda da su. Idan hukuma ce ta gwamnati ko masu zaman kansu, hakan na ba ta damar tsara harkar suna da kalmomin izinin shiga da za ta ko take bai wa ma’aikatanta. Wannan ke sa dukan ma’aikatan kamfanin su mallaki tsarin suna da kalmar izinin shiga mai siffa da yanayi iri daya a karkashin tsari daya.

Wadannan ka’idoji na Imel suna dauke ne da ka’idojin “Password” a daya bangaren. Ba komai wadannan ka’idoji suka kunsa ba illa siffofin da ake so kowane “Password” ya mallaka. Wadannan siffofi kuwa su ne:

Tsawo:

Wannan shi ne iya karancin haruffa ko lambobin da ake so ka sa a matsayin “Password” dinka. Ma’ana, daga haruffan da adadinsu ya kai kaza, misali. A zamanin baya farkon bayyanar Imel, kamfanoni irin su Yahoo da Hotmail da Edcite da American Online (AOL) sun kayyade tsawon “Password” din da dukan mai son bude Imel da su zai kayyade ne. A lokacin nan, dole ne tsawon “Password” ya kai haruffa ko lambobi ko hadakar haruffa da lambobi guda shida (6). A haka lamarin ya ci gaba har zuwa shekarar 2004 ko 2005, lokacin da kamfanin Google ya samar da manhajar Imel dinsa mai suna: Gmail.  Daga lokacin kamfanin Google ya kayyade tsayin “Password” zuwa guda takwas. A takaice dai, wannan tsari na ka’idojin “Password” ne ke sa kamfani ya kayyade yawan haruffa ko lambobin da za a yi amfani da su a matsayin “Password.” Don haka, a yanzu mafi karancin tsayin “Password” shi ne haruffa takwas. Kada ya kasa haka.

Hadaka (Combinations)

Abu na biyu cikin ka’idoji da siffofin “Password” shi ne Hadaka; me da me ake so ka hada don samar da “Password” dinka? A baya kamfanonin Imel da sadarwa a duniya ba su damu da wannan ba, kamar yadda ba su damu da yawan haruffa ba sosai. Amma a karkashin wannan ka’ida ta “Password Policy,” kamfanoni kan sa ka’idoji kan nau’ukan haruffan da suke so a yi amfani da su a matsayin “Password.” Ana son “Password” dinka ya hada da babban harafi (Capital letter) da lambobi, da kuma alamomi – irin su: * , . & ( ) $ # @  – da sauransu.

Tsawon rayuwa (Longebity)

Rayuwar “Password” wani maudu’i ne mai zaman kansa na bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwa, musamman wajen kariyar bayanai. Abin da wannan ke nufi shi ne, daga lokacin da ka zabi “Password” dinka, kwamfutar da ta karbi “Password” din nan take za ta fara kirga kwanakin wannan kalma da ka shigar. A karkashin wannan ka’ida, dole ne ya zama kowane “Password” yana da iya adadin kwanaki (makonni, ko wata, ko shekara, ko shekaru, misali) da aka deba masa. Da zarar ya rage ’yan kwanaki (kamar kwana 10 misali) lokacinsa ya kare, sai kwamfutar ta fara sanar da kai cewa ka canja “Password” din.

Sai dai wannan ka’ida galibi a kamfanonin hukumomin gwamnati ne ko kamfanoni masu zaman kansu. Amma kamfanonin sadarwa na Imel ba su tilasta wannan ka’ida, sai dai su shawarce ka, musamman idan suka fahimci wani na yunkurin sace maka “Password” dinka.  Amma a babin ya-kamata, a duk watanni shida ka rika canja “Password” dinka in da hali. Barin “Password” tsawon zamani ba canji kan sa wani ya sace, ya rika amfani da shi ba ka sani ba. Amma idan kana kan ka’idar lokaci da kake canzawa, duk sa’ar da wani ya sace yana amfani da shi ba da saninka ba, da zarar ka canja shi ke nan, matsalar ta ragu.

Yanayi (Nature)

Wannan shi ake kira “Nature”, wato yanayin da ake so kowane “Password” ya kasance a ciki. Abin da wannan ke nufi shi ne: nau’ukan abin da kowane “Password” ya kunsa – haruffa da lambobi da alamomin rubutu da dai sauransu. Misali, a wasu daga cikin hukumomin gwamnati, ka’ida ce idan ka zo zabar “Password” dole ne ka hada da Babban Harafi (Capital Letter) da lamba da alamomi ko isharorin rubutu na musamman (Special Characters). Kana iya ganin “Password” haka: “Jamilu@2013” ko “Idris12**” ko “Abdul00%%”, misali. Ba su kadai ba, hatta kamfanonin sadarwa masu bayar da Imel a duniya yanzu sun fara amfani da wannan ka’ida. Babbar hikimar da ke cikin yin haka ita ce don tsaurara matakai tare da dakile yunkurin masu sace wa mutane “Password” karfi da yaji. Sai dai kuma, wannan tsari yana da tasa matsalar, kamar yadda mai karatu zai gani nan gaba.

Haramtattun Alamomi (Prohibited Elements)

Wadannan su ne nau’ukan haruffa ko lambobi ko alamomin rubutu da aka haramta amfani da su a matsayin “Password” ko a cikin “Password.” Wannan ka’ida ce da kowane kamfani ko hukuma take da nata tsari a kai. Misali, a wasu ma’aikatun, haramun ne karkashin wannan ka’ida “Password” dinka ya kunshi kalmar “password”, ko alamar “@”, misali. A wasu ma’aikatun kuma haramun ne yin amfani da kalmomin Turanci da ke cikin kamus, wato: “Dictionary Words,” misali.

Wadannan, a takaice, su ne wasu daga cikin ka’idojin “Password” da ake amfani da su a halin yanzu a duniya. Don haka, sai ka yi amfani da wadannan siffofi da ka’idoji wajen zaba ko kintsa “Password” dinka. Don samun kariya daga miyagu.