✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin magance warin jikin ki

Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin mutane. Musamman lokacin zafi idan aka hada gumi ko aka yi yawo…

Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin mutane. Musamman lokacin zafi idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana na tsawon lokaci sai a ji warin jiki na tashi sosai. Ana samun warin jiki ne saboda yanayin gari, wani lokaci ana haifar mutum da shi ko ta irin abincin da muke ci. Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun guso sai a ji tashin tafarnuwar. Don haka a yau na kawo muku hanyar da ita ce mafi sauki don magance wadannan matsaloli.

• Turare: Yawan fesa turare na jiki ko na hammata na rage warin jiki. Amma yawan amfani da su na janyo kyankyami wanda zai sanya kuraje fesowa.

• Sabulu da ruwa: Hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce amfani da ruwa tsabtatacce da sabulu don yin wanka kamar sau uku a rana kuma a dage da wanke lungun da ke janyo wari kamar su hammata da sauransu.

• Tsabtatacciyar riga: Kada a manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan kayan da yake sanyawa masu datti ce to lallai ba za a rabu da warin jiki ba. Don haka ana son ana sanya tsabtatattun kaya musamman kayan da ake sanyawa a karkashin kaya kamar su bireziya da sauransu.

• Amfani da alam: Idan warin jiki ya kasance mai tsanani ne to sai a rika wanka da alam domin rage wari.

• Zuma: Idan an gama wanka za a iya zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi sannan a watsa a jiki hakan na rage warin jiki.

• A sha ruwa: Domin rage warin jiki, a sha kofin ruwa daya da sassafe kafin a ci komai. Yin hakan na rage warin jiki.

• Amfani da ruwan rose (rose water): Za a iya diga ruwan rose a cikin ruwa kafin a yi wanka hakan na rage warin jiki da dada wa jikin kanshi.