✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin rage gumin fuska

An camfa cewa kowane mai yawan gumin fuska musamman ma na hanci,masifaffiya ce ko masifaffe. Gumin fuska a likitance ana kiransa da ‘hyperhidrosis’ shi ne…

An camfa cewa kowane mai yawan gumin fuska musamman ma na hanci,masifaffiya ce ko masifaffe. Gumin fuska a likitance ana kiransa da ‘hyperhidrosis’ shi ne yake sanya yawan gumin fuska; kamar kan hanci, goshi, saman labba, wuya da sauransu. Wani za a gan shi yana da yawan gumi ba tare da ya yi wani aiki ba. Akwai abubuwa da dama da suke sanya gumin fuska kamar ciwon suga, yawan kiba, hawan jini , bacin rai da sauransu.

Mata wadanda suke yawan son kwalliya za su tsane gumin fuska domin kuwa yana bata musu kwalliyarsu. Babu maganin gumin fuska amma akwai yadda za a yi domin a rage shi.

  • A rage cin abinci wanda ya kunshi barkono ko kayan yaji
  • Yawan shan bakin shayi na janyo gumin fuska amma za a iya shan ruwa mai yawa don ya taimaka wajen wanke duk maikon jikin.
  • A rage yin amfani da man shafawa mai maiko domin irin nau’o’in wannan mai, za su dada gumin fuska. A nemi mai marar maiko domin fuska.
  • Cin ’ya’yan itatuwa da ganye kamar; latas, alayyahu da sauransu, za su rage gumin fuska.
  • A samu ruwan ‘binegar’ a hada da zuma mai kyau wadda ba a hada ta da sukari ba, sai a sha sau uku a rana kafin aci abinci.
  • Za a iya samun ganyen ‘mistletoe’ a tafasa shi da ruwa na tsawon minti 15 sai a sha yana rage gumin fuska.
  • Ganyen alkama yana da kyau wurin rage gumin fuska. A tafasa shi a sha ruwansa domin shi ganyen alkama, yana kunshe da sinadarin bitamin C da kuma bitamin B-12 wajen rage maiko da kuma gumin fuska.