✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin samun ruwan sha

Wane ruwa ne ya fi dacewa mutum ya rika sha? Kuma mene ne gaskiya a kan ruwan burtsatse? Na ji ana cewa yafi ruwan roba…

Wane ruwa ne ya fi dacewa mutum ya rika sha? Kuma mene ne gaskiya a kan ruwan burtsatse? Na ji ana cewa yafi ruwan roba kara lafiya dari bisa dari. Mene ne gaskiyar wannan batu?
Daga: Zahra’u Auwal, Kano
Amsa: To, a kimiyance muna da tsatson ruwa iri-iri. Akwai na sama, akwai na teku, akwai na kogi da koramu, akwai na karkashin dutse; akwai kuma na karkashin kasa. Kowane ruwa ana iya shansa ne daidai yawan sindaransa, irinsu sodium, potassium da phosphorous da sauransu da yanayin gurbatar kwayoyin cuta.
Ruwan sama yana samuwa a wasu wuraren a duk tsawon watannin shekara, wasu su samu a rabin shekara, wasu su samu a wasu ’yan ranaku. Kai akwai bangarorin duniyar ma da ba sa ganinsa ko sau daya. Ruwan sama irin namu yana da sinadarai domin sha daidai gwargwado, don haka za a iya tara kai tsaye a sha ba cutarwa. Idan ya biyo ta kan kwano ko indararo zai iya gurbata ko dai da tsatsa ko kura ko kwayoyin cuta. Akwai kuma kasashen da ruwan samansu fa ba ya shawuwa saboda akwai sinadarin acid a cikinsa (acid rain a turance).
Ruwan teku shi ne ya fi kowane irin ruwa mai kwanciya yawa a duniya, domin fiye da rabin duniyar ma teku ce ta mamaye. To sai dai shi kuma sinadarin sodium da chloride sun yi yawa sosai a cikinsa, wato yana da gishiri fiye da yadda jikinmu yake bukata, don haka sai an tace gishirin akan iya sha. Idan an sha ma amai ake yi.
Sinadaran ruwan kogi da na koramu daidai sha ne, sai dai mutane da dabbobi sukan iya gurbata su da kwayoyin cuta, ta hanyar wanka da wanki da ba-haya da sauransu, don haka sai an tace an tafasa, kafin a sha.
Ruwan famfo kan samu ta wadancan kafofi da aka zayyana a sama, walau ruwan sama, wanda akan tara shi a dam misali, ko na kogi, ko na teku a wasu kasashen, sa’annan a tace shi, a gyara shi, a sa magani ta yadda ba zai cutar da al’uma ba. To, a irin kasashenmu inda gizo ke saka a maganar ruwan famfo, shi ne ta fashewar bututun ruwa a kan hanyoyinsu na zuwa gidaje da masana’antu, inda kwayoyin cuta kan shiga su fita a duk lokacin da suka ga dama.
Sai maganar burtsatse, wanda shi ne ruwan karkashin kasa ko ruwan rijiya mai zurfi sosai kuma mai murfi, wadda ake diban ruwanta da inji a kai sama a ajiye a tankuna ko da injin tuka-tuka. Duk rijiyar da ba ta cika wadannan ka’idoji ba, sai an tafasa ruwanta kafin a sha.
A iya cewa E, za ta iya yiwuwa ruwan burtsatse ya fi na robar sayarwa kyau, domin da wuya a samu kwayoyin cuta sun gurbata ruwan burtsatse. Wasu masu ruwan robar sayarwa da yawa ma ruwan burtsatsen suke gyara wa dandano su zuba a roba, wasu kuma su tsabtace na famfo su kara sinadaran kashe kwayoyin cuta su sayar.
Amma fa akwai ruwan roba da ake samu wanda shi ma daga karkashin dutse yake bubbugowa kuma kai tsaye ake zubawa a robar sayarwar, ba a kara komai. Wato dai ruwa ne tsabtatacce shi ma, kamar ruwan burtsatse koma fiye. dan bambancin da za a samu shi ne bambanci kadan na sinadaran cikin rowan, wanda wannan ya danganta da mazaunin dutsen ko rijiyar. Sindaran da akan samu a irin garuruwan Sokoto da Kebbi da bambanci a kan wadanda za a samu a Jihar Filato, haka na Filato suna da dan bambanci da na Kano, a misali.
Wai shin likita wane ciwo ne yake sa saman kafafu su kumbura amma ba ciwo? Shin sanyin kashi ne ko dai wani abu ne daban? A yi min bayani.
Daga Ali Garba, Okene
Amsa: To, tun da mun yi bayanin ciwon sanyin kashi a makon da ya gabata kuma mun ce sanyin kashi zai iya sa kumburin kananan gabobi musamman na kafa, ya kamata a bambance kumburin kafa na gabobi da na dukkan kafar ko saman kafa kamar yadda ka tambaya.
Shi irin wannan kumburi ba irin na ciwon sanyin kashi ba ne, shi ruwan jiki ne wanda ya yi yawa yake saukowa ya taru a kafafu a karkashin fata, ba a gabobi ba. Akwai matsaloli ke nan daban masu sa haka. Wadannan su ne duk cututtukan da ka iya sa ruwan jiki ya taru wato irinsu ciwon koda, ciwon zuciya, ciwon hanta da ciwon daji. Ba za kuma a iya ganin kumburin kai tsaye a ce e, ciwon koda ne ko na zuciya ba har sai an yi aune-aune da gwaje-gwaje.
Wane magani ya kamata mai ciwon sanyi wanda ke fitar da farin ruwa ya sha?
Daga Sunusi Dogaro Ga Allah
Amsa: Ba magani ake sha kai tsaye ba, tuntubar cibiyar lafiya mafi kusa ake yi tukun a yi gwajin farin ruwan ko fitsari kafin a sha magani.
Ni mai bibiyar wannan fili ne a koyaushe. Ina son likita ya ba ni shawara domin na yi fama da cutar TB. Bayan na sha magani wata takwas, an tabbatar min na warke. To har yanzu ina jin wasu alamu na wahala wurin numfashi da kuma jin wani abu yana yawo a jikina. Da fatan zan samu shawara.
Daga Mustafa, Gusau
Amsa: To abin da ke faruwa suna da yawa, a mafi yawan lokuta ana shan magungunan tari a warke gaba daya, ko da na wata shida ne, wasu lokuta kuma ana shan maganin ciwo ya lafa amma daga baya ya dawo, wato bai tafi gaba-daya ba. To a irin wannan yanayi sai an canza magani, mai hade da allurar wata daya, an bayar na tsawon wata takwas. A wasu lokuta kuma akan sha magani a warke gaba daya, daga baya wani sabon ciwon ya shiga.
To koma dai mene ne yake faruwa, ba a nan za a ce ka warke ko ba ka warke ba, ko ka warke ka sake samun sabon ciwo, a cibiyar da ka sha maganin za a tantance wadannan bayan ka sake gwaje-gwaje.
Ina son a yi man karin bayani ko mace na iya kamuwa da cutar TB ta hanyar saduwa da mai tarin?
Daga Fati, Gusau
Amsa: A’a, mun sha fada a wannan shafi cewa ta hanyar shakar kwayar cutar a iska idan mai ciwon ya yi tari ake daukar wannan ciwo. Don haka ciwon TB ba ciwon sanyi ba ne, wanda za a ce za a iya dauka ta hanyar saduwa.

LAFIYAR MATA DA YARA

Doguwar nakuda

Haihuwata hudu kuma duk sa’ar da na fara nakuda nakan yi awa 30-32 cikin matsanancin yanayi. Wannan ne ke sa ni fargaba da zullumi duk sa’ar da nake da ciki. A haka ma wata jaririyata ruwan mahaifa ya cika mata ciki, kwana 2 ta rasu. Idan na ce a yi min tiyata sai a ga kamar ban san ciwon kaina ba. Maigidana ma yana ganin na hakura da haihuwar, ni kuma ina son na kara.
To shin ba wani taimako da ake ba mai nakuda ta haihu a awa goma ko kasa da haka? Ko abin da zai rage radadi da ciwon nakuda?
Daga Maman Al-Ameen, Kano
Amsa: kwarai kuwa nakudar da ta wuce awa 14 ta wuce misali kuma tabbas shan ruwan mahaifa a jariri yana daya daga cikin alamu na doguwar nakuda. Ita doguwar nakuda ta fi jawo salwantar ran jariri fiye da na uwa, duk da cewa takan jawo wa uwa galabaita sosai don takan iya sa ciwon yoyon fitsari ma.
Duk asibitin da suka san me suke yi, bai kamata ma a ce ke ce za ki gaya musu cewa tiyata kike so ba. Kamata ya yi da an ga kin fara tagayyara a nemi dabara, a san yadda aka yi kika yi sauri kika haihu, ko dai ta hanyar allura (allurar ruwan yaji din nan) ko ta hanyar yin amfani da hannu ko inji wajen jawo abin da ke ciki din, ko ma ta hanyar tiyata. Wato kafin a je tiyata sai an duba an ga ko za a iya gwada wadannan abubuwa tukuna, idan abu ya gagara, to a wannan lokaci sai an shiga tiyata tabbas. Duka-duka wannan shi ma bai fi ya ci awa biyu zuwa uku ba. Wannan shi ne taimakon da ya kamata a ba duk wata wadda aka ga nakudarta ta fara tsayi. Watakila da asibitin kudi kika je kika ce ga abin da kike so, idan mai yiwuwa ne na san su ba bata lokaci akan samu biyan bukata daidai gwargwado.
A bangaren tambayarki ta biyu kuma, inda kika ce ko ana ba da maganin rage zafin nakuda, tabbas akwai sai dai har yanzu ban ji asibitin da suka fara ba da irin wannan magani ba a nan kasar. A kasashen da suka ci gaba da mace ta ce tana so dole a ba ta. Yawanci allura ce ake yi a gadon baya. Wasu matan suna ganin da zafin allurar gadon baya gara a bar su da zafin nakudarsu. daya hanyar kuma ita ce ta sa wa mace iskar entonod a hanci, wadda za ta sa duk lakar mai daukar zogi jin zafi. To ban sani ba ko don tsadarsu ne ba a yi a kasar nan, tun da suna da ’yar tsada.
Kai tun kafin nakudar ma ta zo, inda aka ci gaba, mata da yawa sukan iya sayen na’urar rage zogin nakuda (TENS machine), wadda ake daurawa kamar guru a ciki don hana zogi. Akwai kuma wata dabara ta shiga ruwa, kamar ruwan a babban bahon wanka na ban daki, shi ma yana taimakawa wajen rage zogi.