Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Har mutanen da suka mutu suna karban albashi a jihar Nasarawa

Wani kwamiti da Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta kafa don gudanar da bincike akan jinkiri da ake samu wajen biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar ya sanar cewa ya gano sunayen wa su mutane da suka mutu da wadanda suka bar aiki a jerin sunayen masu karban albashi daga dukkan kananan hukumomin jihar.

Shugaban majalisar dokokin Ibrahim Abdullah Balarabe ne ya bayyana haka jim kadan bayan ya karbi rahoton da shugaban kwamitin Mohammed Alkali da ke wakiltar mazabar Lafiya ta Arewa ya gabatar masa. Yace rahoton da kwamitin ya gabatar masa ya gano kura-kurai da dama a harkokin kananan hukumomin ciki har da na karin girma ba bisa ka’ida ba da yin amfani da sunaye fiye da daya wajen karban albashi da sauransu. Ya ci gaba da bayyana cewa “Bayan kwamitin ya gano cewa akwai sunayen wasu mutane da suka mutu da dadewa da wadanda su ka bar aiki a jerin sunayen wadanda ke karban albashi daga dukkan kananan hukumomi 13, kwamitin ya gano cewar a halin yanzu kananan hukumomi 4 ne kacal da suka hada da Awe da Keffi da Keana da Wamba ka iya cigaba da biyan cikakken albashin ma’aikatansu ya yin da sauran kananan hukumomi 9 basa iya biya cikakken albashin Saboda facaka da kudi ta hanyoyi da basu dace ba da ake yi.

ADVERTISEMENT

Shugaban             Majalisar ya yi Allah-wadai da aukuwar lamarin wanda a cewarsa ke shafar harkokin kananan hukumomin da jihar baki daya, inda nan take ya umurci dukkan Shugabannin kananan hukumomin suyi wani abu akan lamarin cikin gaggawa don magance shi.

Tun farko a jawabinsa shugaban kwamitin Hon Ibrahim Alkali, ya  bukaci majalisar ta kara musu lokaci don basu damar kammala binciken. Yace “Har yanzu bamu samu damar ziyartar wasu kananan hukumomin ba, Saboda karamcin lokaci kuma akwai abubuwa da dama da mu ka gano a ya yin bincikenmu da mu ke so mu tabbatar.” Idan ba a manta ba a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar ta kafa wannan kwamitin mutum 6 don gudanar da cikakken bincike akan jinkiri da ake yawan samu wajen biyan albashin ma’aikatan duka kananan hukumomin jihar 13 da wasu kudade da ake cire dga albashinsu ba bisa ka’ida ba. Tuni dai Majalisar ta amince da karawa kwamitin makonni 3 don basu damar ci gaba da gudanar da cikakken bincike da neman hanyoyi da zasu kawo canji mai ma’ana a kananan hukumomin.

ADVERTISEMENT